Ni ban matsa dole sai na zama shugaban ƙasa ba – Atiku

0
355
Ni ban matsa dole sai na zama shugaban ƙasa ba - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar

Ni ban matsa dole sai na zama shugaban ƙasa ba – Atiku

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa burinsa shi ne ganin Najeriya ta samu shugabanci nagari da ci gaba, ba wai sai ya zama shugaban ƙasa dole ba.

Atiku, wanda Farfesa Ola Olateju ya wakilta a wajen taron karɓar sababbin ‘yan jam’iyya da suka koma ADC daga PDP da LP a Legas, ya ce ADC yunkuri ne na neman sauyi, ba kawai jam’iyya ba.

Ya bayyana cewa burinsa shi ne ganin Najeriya ta samu shugabanci mai inganci, wanda zai tabbatar da tsaro da walwala ga ‘yan ƙasa, ba wai lamari na kashin kansa ba.

KU KUMA KARANTA: Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga PDP

Game da zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a 2027, Atiku ya ce za a bar wa jama’a ta hanyar sahihin zaɓe, inda ya jaddada cewa babu wanda za a tilasta wa a matsayin ɗan takara.

A cikin sababbin da suka sauya sheƙa zuwa ADC akwai tsohon shugaban PDP na Legas, Cif Muritala Ashorobi, Rt. Kyaftin Tunji Shelle, da Dr. Abimbola Ogunkelu, yayin da suka samu tarba daga jagororin jam’iyyar ciki har da Ogbeni Rauf Aregbesola.

Leave a Reply