Netanyahu ya tsallake rijiya da baya – Isra’ila

0
92
Netanyahu ya tsallake rijiya da baya - Isra'ila

Netanyahu ya tsallake rijiya da baya – Isra’ila

Gwamnatin Isra’ila ta ce, wani jirgi marar matuƙi ya kaikaici gidan Firaiminista Benjamin Netanyahu a ranar Asabar, ba tare da wani ya jikkata ba, yayin da babu wata alama tayin sanya a faɗan da take ci gaba da gwabzawa da dakarun Hezbollah na Lebanon, da na Hamas dake Gaza, kan kisan gillar da Isra’ila ke yi a Gaza.

Sojojin Isra’ila sun ce, an ƙaddamar da gwamman hare hare daga Lebanon, kwana guda bayan Hezbollah ta sanar da buɗe wani sabon babi a faɗan. Ofishin Netanyahu ya ce, harin jirgi marar matuƙi ya kaikaici gidan sa ne dake garin Caesarea dake yankin gaɓar ruwan mediterreniya. Daga shi har matar shi dai ba sa cikin gidan a lokacin, babu kuma tabbacin ko harin ya samu gidan.

Netanyahu ya ce, ‘a yau ‘yan koren Iran da suka yi ƙoƙarin hallakani da mai ɗakina sun tabka mummunan kuskure’.

Hezbollah dai ba ta ɗauki alhakin harin jirgi marar matuƙi ba, to sai dai ta ce, ta kai hare haren rokoki a arewaci da tsakiyar Isra’ila. Harin ya zo ne a daidai lokacin da aka yi hasashen Isra’ila za ta maida martani ga wani hari da Iran ta kai a farkon watan nan, wadda ke marawa Hezbollah da Hamas baya.

KU KUMA KARANTA:Yadda Isra’ila ta kashe shugaban Hamas Yahaya Sinwar

A nata ɓangaren, Isra’ila ta kai aƙalla hare hare ta sama 10 a kewayen kudancin Beirut da aka sani da Dahiyeh, yanki mai shakare da jama’a inda ofisoshin Hezbollah suke, cewar hukumomin Lebanon. Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hari kan wuraren Hezbollah.

A can Gaza kuwa, mayaƙan Isra’ila sun kai hari kan asibitoci a kewayen arewacin Palasɗinu da aka yi fata-fata da shi, haka zalika, hare hare ya kashe mutane sama da 50 da ya haɗa da ƙananan yara a cikin ƙasa da sa’oi 24, cewar jami’an asibiti da wakilin kafar yaɗa labarum Associated Press dake yankin.

‘Har yanzu yuwuwar ɓarkewar yaƙi a yankin na ci gaba da zama abin damuwa matuƙa’ cewar ministan harkokin wajen kasar Parisa wato Iran Abbas Araghchi, a lokacin da ya ziyarci Turkiyya. Wani ayarin ministocin tsaron su 7 yayi gargaɗin rincaɓewar al’amurra da shiga yaƙi gadan gadan. Tuni dai kashen Amurka, Birtaniya da sauran ƙasashen yamma suka aiyana Hamas da Hezbollah a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci.

Leave a Reply