Ndume: Saraki ya ci amanata a majalisa

0
35
Ndume: Saraki ya ci amanata a majalisa

Ndume: Saraki ya ci amanata a majalisa

Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Kudancin Borno, ya ce Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ci amanarsa duk da ƙoƙarin da ya yi na ganin ya zama shugaban majalisar.

Da yake magana da sashen Hausa na Deutsche Welle (DW), Ndume, ya bayyana yadda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Saraki, ya juya masa baya duk da goyon bayan da ya bashi wajen zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 8.

“An tsige daga matsayin Shugaban Majalisar Dattawa sannan aka dakatar da ni na tsawon wata takwas ba tare da albashi ba.

“Wannan ya baƙanta min rai saboda mun yi ƙoƙari wajen ganin Saraki ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, amma ya ci amanata.

“Kwanan nan ma an cire ni a matsayin tsawatarwa saboda faɗin gaskiya. Amma yanzu wannan ya wuce, kuma ina ganin Allah yana ɗaukar fansa kan wannan cin amana.”

KU KUMA KARANTA: Babban matsalar Najeriya shi ne cin hanci da rashawa ; Ndume

Ndume, ya kuma bayyana damuwarsa game da halin da talakawa ke ciki a Najeriya duk da ƙoƙarinsa na ganin an inganta rayuwarsu.
Ya ce dimokuraɗiyya a ƙasar nan ta rasa ma’anarta.

“Yana daga min hankali cewa duk da ƙoƙarin da nake na tallafa wa rayuwar talakawa, ba a samu canji ba.

“Muna da babban buri a lokacin mulkin Buhari har ma da wannan gwamnati mai ci, muna tunanin cewa sadaukarwar talakawa za ta samar da mafita. Ina cikin damuwa saboda ni ma ɗan talakawa ne.

“Yanzu gwamnati ta koma yin abun son rai. Gwamnatin dimokuraɗiyya ya kamata ta zama ta mutane, don mutane, kuma daga mutane. Amma ba haka abun yake a yanzu ba.”

Leave a Reply