NDLEA ta sami lambar yabon rage shaye shayen miyagun ƙwayoyi a Borno

1
489

Shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (Murabus) ya bai wa hukumar NDLEA reshen jihar Borno lambar yabo a matsayin wanda ya yi nasara a kan ƙwazon da ya nuna wajen rage shaye shayen muggan ƙwayoyi, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Kwamandan rundunar na jihar Borno ne ya karɓi lambar yabon, Mista Joseph Icha a lokacin taron Hukumar na shekarar 2022 da aka yi a bikin karramawa da bada lambar yabo na hukumar NDLEA ta ƙasa da ya gudana hedikwatar hukumar da Abuja a ranar Talata 20/12/2022.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar a jihar Borno Segun Jokaoso ya sanyawa hannu ya bayyana cewa kwamandan jihar wanda Mataimakin Kwamanda na jihar ya raka, wato Abdullahi Sardauna ya godewa shugaban hukumar ta NDLEA bisa yadda ya amince da gudanar da ayyukan hukumarsa a matsayin kwamandan kwarya-kwaryar gudanar da ayyukanta na rage shaye-shayen kwayoyi a fadin jihar.

Kwamandan na jihar ya kuma tabbatar da ƙudurinsa na tabbatar da cewa an daƙile yawan shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a jihar Borno.

Joseph Icha, ya jaddada cewa ayyukansa tare da bada umurninsa waɗanda suka sa aka bayar da kyautar, sun haɗa da; Ilimin rigakafi na shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ba da shawara, gyara, wayar da kan jama’a, faɗakar da jama’a, faɗakarwar al’umma, bayar da shawarwari, amfani da kafafan yaɗa labarai, da sauransu.

Ya kuma kara nanata cewa wanda aka baiwa abu mai yawa ana sa ran yayi aiki tuƙuru don haka ya tabbatarwa mutanen jihar Borno ayyuka masu kyau da za su taba rayuwar ‘yan ƙasa da ƙarfafa masu gwiwa.

Duk wanda zai shiga cikin yaƙin da ake yi na yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar Borno

Kwamandan ya sadaukar da lambar yabon da ya samu ga mutanen jihar Borno da jami’an tsaro daban-daban na jihar domin hadin kai da suke bai wa rundunar ta NDLEA.

1 COMMENT

Leave a Reply