NDLEA ta kama maniyyata a filin jirgin saman Kano, bisa zargin safarar hodar Iblis zuwa ƙasar Saudiyya
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar NDLEA ta kama wasu maniyyata biyu a filin jirgin saman Malam Aminu Kano bisa zargin safarar hodar iblis zuwa Saudiyya yayin aikin Hajji.
Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a Lahadin nan, 1 ga Yuni, 2025.
KU KUMA KARANTA: Al’ummar Gwammaja a Kano sun shiga jimamin tunawa da rashin da sukai na faɗuwar Jirgin sama a yankin
Sanarwar ta ce an samu maniyyatan da hodar iblis har guda 45 kowanne, kuma bincike ya gano cewa wasu mutane uku ne ke daukar nauyin safarar da nufin amfani da mahajjata wajen aikata laifin.









