Gwamnatin Kano ta sanar da ranar hutun Babbar Sallah ga makarantun jihar
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan makarantun Firamare da na Sakandare a fadin jihar da su tafi hutun Babbar Sallah daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025 zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban makarantu kwana, sannan daga ranar Laraba 4 ga Yuni, 2025 zuwa Litinin 16 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban da ke zuwa gida bayan makaranta.
KU KUMA KARANTA:Nijar ta dakatar da fitar da dabbobi zuwa ƙetare a gabanin sallah
Wani jawabi da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu ya bayyana cewa iyaye da masu kula da ɗaliban makarantun kwana su je su ɗauki ‘ya’yansu da sassafe a ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta rawaito Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda yana kira ga iyaye da masu kula da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun dawo makaranta a ranar da aka tsara, tare da gode musu bisa goyon baya da hadin kai da suke bai wa ma’aikatar.