Gwamnatin Tarayya ta miƙa ƙoƙon bara na neman taimako da haɗin kan Faransa domin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta dabaibaye ƙasar.
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan yayin wata ganawar sirri da ya yi da wasu ’yan majalisa da kuma jami’an hukumomin tsaron Faransa a yammacin wannan Talatar.
Ministan a yayin taron wanda Gassillound Thomas ya jagoranci wakilan Faransa a Abuja, ya buƙaci su kawo wa Najeriya ɗauki domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro da suka addabi ƙasar.
A cikin sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Najeriya, Henshaw Ogubike ya fitar, ministan ya ce akwai bukatar a inganta alakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa ta fannin kayan aikin soji da horar da jami’an sojin ƙasar.
KU KUMA KARANTA: Wike ya ƙira taron gaggawa kan matsalar tsaro a Abuja
“Ina da yakinin cewa Gwamnatin Faransa za ta iya tallafa wa Najeriya da kayan aiki domin daƙile matsalar tsaro da tada ƙayar baya.
“Kun dai sani cewa Najeriya tana da ɗimbim al’umma da saboda haka idan akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali, tarin al’umma zai taimaka mana wajen bunƙasar tattalin arziki,” kamar yadda Ogubike ya ruwaito Ministan na cewa.
Badaru ya ce Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu za ta yi amfani da hanyoyin da suka dace wajen ganin ta kawar da makiya da ke tayar da kayar baya a sassan ƙasar nan.
Tsohon Gwamnan na Jihar Jigawa ya ƙara da cewa, tun bayan zamansa ministan tsaro, ya yi ganawa har sau uku da Faransa a fannin haɗin gwiwar soji, yana mai cewa “wannan yana nuna kyakkyawar alaƙar da muke da ita da Faransa”.
Ya kuma yaba wa dangantakar da ke tsakanin majalisar dokokin Faransa da ta Najeriya, inda ya ce irin wannan haɗin kan zai bunƙasa yaƙi da matsalar tsaro.
Da yake jawabi, Shugaban Majalisar Faransa, Mista Gassiloud Thomas, ya ce gwamnatinsu za za ta tallafa a wasu fannonin da Ministan Tsaro ke ganin gwamnatin Faransa za ta iya taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da matsalar tsaro.
“Tabbas muna yabawa da rawar da kuke takawa wajen ƙarfafa dangantakar, kuma za mu ci gaba da tallafa wa wannan gwamnati mai ci domin daƙile matsalar tsaro.
“Wannan alaƙar tana da matuƙar muhimmanci domin Najeriya na da tasirin gaske dangane da irin rawar da take takawa wajen daƙile matsalar nahiyyar Afirka.”