Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.3 don kammala layin dogon Kano zuwa Maraɗi

0
168

Gwamnatin Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.3 domin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi da ke Jamhuriyyar Nijar.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ta yi a ranar Laraba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa kamfanin gine-gine na ƙasar China, CCECC, ne zai samar da kaso 85 na kuɗaɗen da ake buƙata.

Haka kuma, ma’aikatar ta ce Gwamnatin Najeriya da haɗin gwiwar Bankin habaka tattalin arzikin Afirka na Africa Development Bank ne ke ɗaukar nauyin aikin.

KU KUMA KARANTA: Nijar ta gaza biyan bashin da ya kai dala miliyan ɗari biyar – WAEMU

“Samun bashin na dala biliyan 1.3 na nuna irin nasarar da za a samu wajen kammala layin dogon,” in ji sanarwar.

Wannan dai na ɗaya daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin Najeriya na inganta harkar sufuri a faɗin ƙasar domin bunkasa tattalin arziki da ke fama da masassara.

Leave a Reply