No menu items!

Sample Page Title

Date:

Najeriya na fafutukar samun kujerar dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya

Yayin da ya ke wakiltar shugaba Bola Tinubu a babban taron majalisar karo na 80 a birnin New York na Amurka, mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya gana da babban sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres a shalkwatar majalisar.

BBC ta rawaito cewa cikin wata sanarwa da ofishin Shettiman ta fitar ta ce shugabannin biyu sun tattauna batutuwa da dama masu muhimmai ciki har da ƙudirin Najeriya na samun kujerar dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.

A lokacin ganawar, Shettima ya ƙarfafa buƙatar Najeriya na neman goyon bayan Majalisar Dinkin Duniyar don cimma ƙudirin nata na samun kujerar dindindin a kwamitin tsaro na majalisar.

KU KUMA KARANTA: Mutane miliyan 31 za su faɗa cikin yunwa matsananciya a Najeriya – Majalisar Ɗinkin Duniya

Shugabannin sun kuma tattauna batutuwan ƙarfafa cimma muradun ƙarni, da sauyin yanayi da ƙararra dimokradiyya a Najeriya da ma yankin Afirka.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...