Mutum ɗaya ya mutu, biyu sun jikkata a wani haɗarin mota a Ogun

0
300

Mutum ɗaya ya mutu, biyu kuma sun jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a safiyar Laraba a kan hanyar Ota-Idiroko.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Anthony Uga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Shugaban FRSC ya ce hatsarin ya rutsa da wata ƙaramar mota ƙirar blue mai lamba BDG 340 XZ, wata babbar mota ce wadda ba ta da lambar rajista, da kuma IVECO Tipper mai lamba AAA 969 ZY.

An ruwaito cewa ƙaramar motar da babbar motar da ba ta da lambar rajista sun kutsa kai cikin titin IVECO Tipper a tsaye a daidai lokacin da suke gangaro wa kan wani gangare a gefen Idiroko na gadar Arobiye, a gadar Iju.

KU KUMA KARANTA: Malaman Addinin Islama 6 Sun Rasu A Hadarin Mota A Kano

Uga ya ce motocin biyu sun kutsa cikin kogin, wanda ya yi sanadin jikkatar mutum ɗaya da kuma wasu mutane biyu da suka samu munanan raunuka.

Shugaban na FRSC ya alaƙanta musabbabin hatsarin da wata matsala ta inji.

Uga ya buƙaci direbobin manyan motoci da su tabbatar da cewa motocin nasu suna cikin koshin lafiya kafin a ɗora su akan babbar hanya.

Leave a Reply