Mutum uku sun rasu wasu 10 sun samu raunukan harbi a rikicin sojoji da direbobin baburan A Daidaita Sahu a garin Gashuwa, Ƙaramar Hukumar Bade ta Jihar Yobe.
A ranar Lahadi ne aka ba hamata iska bayan wata motar sojojin rundunar Operation Hadin Kai da ke aikin sintiri ta yi taho-mu-gama da wasu masu baburan, inda wani direban baburin da fasinjojinsa suka samu raunuka.
Hatsarin da ya auku a Gadar Gashuwa da ke kusa da garin ya fusata jama’ar yankin inda suke zargin sojojin da gudun wuce kima da tukin ganganci da kuma rashin bin dokar hanya.
Wani shaida ya bayyana cewa a sakamakon haka ne matasa waɗanda akasarinsu masu baburan ne suka fara zanga-zanga, suka tare babban titin zuwa Gashua.
“A sakamakon haka ne sojoji suka mayar da martani ta hanyar yin harbi, har aka samu rasuwar mutum ɗaya a wurin,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: Shugaban mulkin sojan Nijar ya tattauna da Putin kan haɗin gwiwar tsaro
Wani ganau kuma ɗan jarida da ya nemi sa sakaya sunansa ya ce hukumomin Asibitin Kwararru da ke Gashua sun tabbatar da rasuwar mutane uku daga cikin waɗanda aka harba.
Ɗan jaridan ya ƙara da cewa wasu mutum 10 sun samu raunuka daga harbin da sojojin suka yi, yawanci a kafafunsu.
Mataimakin kakakin Rundunar Operation Hadin Kai da ke Damaturu, Kyaftin Shehu Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce suna jiran rahoton jami’insu da ke kula da yankin da abin ya faru.
Sanata Ahmad Lawan, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, ya buƙaci hukumomin soji su binciki lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace.