Muna da ɗalibai 350, amma malamai uku kacal muke dasu – Al’ummar Gabchyari ta jihar Bauchi

2
686

Al’ummar Gabchyari da ke ƙaramar hukumar Darazo ta Jihar Bauchi, sun ce makarantar firamare da ƙaramar sakandare JSS ɗaya tilo a yankin mai yawan ɗalibai 350, amma tana da malamai uku kacal.

Wasu daga cikin al’ummar yankin ne suka bayyana hakan a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Gabchyari a ranar Litinin.

Sun ce lamarin ya taimaka wajen yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin, sun kuma yi ƙira ga gwamnatin jihar Bauchi da ta tura ƙarin malamai a makarantar domin ceto lamarin.

KU KUMA KARANTA: Jami’ar ATBU ta hana shigar nuna tsaraici ga ɗalibai

Ɗaya daga cikin al’ummar garin Malam Isa Ibrahim ya ce matsalar ƙarancin malamai a makarantar ya kuma hana iyaye da dama sanya ‘ya’yansu makaranta.

Ya ƙara da cewa “Muna son gwamnati ta taimaka mana wajen samun ƙarin malamai a nan, malamai na da matuƙar muhimmanci kuma ana buƙatar su a wannan makaranta.”

Hakazalika, wani mazaunin garin Yahaya Adamu, ya yi ƙira ga gwamnatin jihar da ta gyara makarantar, domin samar da muhallin da ya dace na koyo da koyarwa.

Ya bayyana cewa a cikin tubali uku na ajujuwa shida da ke makarantar, biyu ne kawai suke da kyau.

Malam Adamu ya ƙara da cewa rashin ruwan sha a cikin al’umma ya taimaka wajen rashin tarbiyyar ɗalibai da iyaye wajen koyo.

“Yana da matuƙar wahala ɗalibai su samu ruwa kafin su je makaranta, sukan shafe lokaci suna neman ruwa a lokutan makaranta.

“Hakan ya sa ba sa zuwa karatu a kan lokaci. Kuma ko da sun je, kullum sun gaji da wahalar ɗebo ruwa,” inji shi. Abdullahi Muhammad, malami, ya ce makarantar tana da malamai biyu ne kawai na azuzuwan JSS, ɗaya na ɓangaren firamare.

“Wani lokaci, mutane suna tambayar mu ‘me kuke koya musu, saboda ku malamai uku ne kawai a makarantar’.

“Muna da malami ɗaya wanda ya zama shugaban makarantar da ɗalibai sama da 200 a makarantar firamare da ɗaliban JSS 150.

“Yawancin lokaci, ni da abokin aikina a JSS muna taimaka wa koyarwa a azuzuwan firamare. Mun je can ne don yin iya ƙoƙarinmu,” inji shi.

Da yake mayar da martani, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Ilimi ta bai-ɗaya ta Jihar Bauchi, Abdullahi Muhammad, ya bayyana cewa tura malamai nauyi ne da ya rataya a wuyan sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomi.

2 COMMENTS

Leave a Reply