Muna da ‘yancin mallakar muhalli don gudanar da rayuwarmu – Martanin almajiran Shaikh Zakzaky ga El-Rufai

Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky da aka fi sani da ‘yan shi’a a garin Zariya sun tashi cikin jimamin rushe musu makarantu da hukumar tsara birane ta jihar Kaduna wato KASUPDA tare da gamayyar jami’an tsaro suka yi a cikin dararen ranakun Lahadi, Litinin da Talata.

Shaikh Abdulhamid Bello, wanda ya kasance shi ne wakilin ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na garin Zariya da kewaye shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya ƙira a ranar Talatar 23 ga watan Mayun 2023 a ɗaya daga cikin muhallin da aka rusa musu wanda ke Babban Dodo a cikin garin Zariya.

Shaikh Abdulhamid Bello ya ce gwamnatin ta Kaduna a karkashin El-Rufai ta rusa musu makarantu guda uku a Zariyan da ya haɗa da makarantun dake Babban Dodo Zariya da na Dogarawa a Sabon Garin Zariya da kuma na Samaru.

KU KUMA KARANTA: Zan ci gaba da korar ma’aikata, da rushe gine-gine har zuwa rana ta ƙarshe a ofis – El-Rura’i

Shaikh Abdulhamid Bello ya fara ne da cewa; “maƙasudin ƙiran wannan taro domin gabatar da bayanai na gaggawa bisa ga abubuwan da suke faruwa ko kuma suka faru suna ma kan faruwa a wannan gari na Zariya ko ma na ce a jihar Kaduna gaba ɗaya.

“Kamar yadda ‘yan’uwa musamman ‘yan jarida suka sani tun wancan makon an samu wata takarda da ta fito daga ɓangaren ma’aikatar tsare gine-gine wato KASUPDA na cewa akwai wasu wurare da za su yi rusau. Duk da mun ɗauki matakai na ƙalubalantar wannan har zuwa kotu da sauran su haka sai dai kawai muka ga kwatsam ana cikin wannan jimamin sai suka fara wannan rusau kwana biyu a Kaduna, sannan kuma jiya da daddare ƙarfe 1 da kwata na dare suka dira”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “wannan makaranta ta Fudiyyah Babban Dodo Zariya sun taɓa rusata, to amma dai ba a fasa yin karatu a cikinta ba. Jiya da daddare suka zo kamar yadda kuke gani suka ƙara zubar da ginin wucin gadin da aka maida. To wannan ba su tsaya a nan ba, suka wuce kuma wata makaranta irin makamancin wannan a Dogarawa dake Sabon Garin Zariya suka rusata. Suka kuma wuce irin makamanciyarta dake Samaru suka rusa”, ya tabbatar.

Shehin Malamin ya ce a yayin rushe musu makaranta a Samarun Zariya, jami’an tsaron sun yi harbe-harbe inda suka harbi “‘yan’uwanmu har guda biyu yanzu suna asibiti”, in ji shi.

Malamin ya ƙara da cewa; “a nan ma sun yi harbi, amma ba su harbi kowa ba. Sun firgita mutanen gari da harbe-harbe. Jiya kusan dai ba a samu baccin kirki a nan cikin gari ba da kuma can Dogarawa da kuma Samaru, sun tada ma al’umma hankali”.

Ya yi ƙira ga al’umma da su fahimci cewa wannan abin da ake musu ta’addanci ne kuma zalunci ne. “Kuma shiru da zalunci idan ana yinsa kamar yarda da shi ne. Shi ya sa dole ainihin al’umma mu tashi mu nema ma kawukanmu haƙƙoƙinmu”.

“Idan mutum ya saurari jawabin da wani wai Kakakin KASUPDA ya faɗi wai ko mutum yana da izini na mallakar gida suna da dama saboda wasu ‘yan dalilai na tsaro wanda bai bayyanar da dalilai na tsaron ba suna iya zuwa su rusa muhalli. Ban san lokacin da KASUPDA suka zama masu tabbatar da tsaro a cikin al’umma ba?’ ya tambaya.

Ya ƙara da cewa; “Sannan kuma a zo gidan mutum, ko muhallin da mutane ke karatu a zo kawai babu sanarwa a shiga a rusa kamar yadda ake yi a wannan jiha, ban taɓa ganin irin wannan ba. An yi waɗannan abubuwa tun cikin shekaru takwas ɗin nan na mulkin wannan El-Rufai, amma kuma al’umma kamar ba su ɗauki mataki akansa ba”.

Ya yi tir da Alla-wadai da rushe-rushen da aka yi musu inda ya ce ba su yarda ba. “Kuma wannan abin ba zai hana ya zama mu ci gaba da rayuwa ba. Tunda idan dai ba zai zo ya ɗauki rayuwarmu. Za mu rayu ne ‘ya’yanmu ba za su yi karatu ba? Za mu rayu ne ba za mu mallaki gidajen da zamu zauna a ciki ba?”, ya tambaya.

“Daga cikin irin ƙarin rahotannin da muke samu shi ne akwai wasu gidajen ɗaiɗaikun da suke son su ƙara rusawa a rubuce. Daga cikin gine-ginen da suka ce za su rusa guda 48, to idan ni ɗan shi’a ne shi ke nan ba ni da ‘yancin na mallaki gida? A dokar Nijeriya ko a dokar jihar Kaduna? Bani da ‘yancin na rayuwa, bani da ‘yancin na mallaki makaranta bisa ƙa’idoji da dokokin jiha da dokokin ƙasa don ba a sona ba a son a aƙidata, ba a son abin da nake yi?”, ya sake tambaya.

Ya ci gaba da cewa; “Wannan yakamata mutane su sa hankali su fahimci cewa abin da ake yi ɗin nan, abu ne da ya saɓawa hankali, ya saɓawa doka, ya saɓawa ƙa’idar addini baki ɗaya”.

Ya ce babu wata takarda da suka bayar na cewa za su yi rusau kawai sun zo ne suka fara rushe-rushen. “Ko wancan takardar a cikin asiri aka samo ta na cewa za a yi rushe-rushe wanda har aka buga a jarida. Amma su aika cewa za su zo ko ku kau da kayanku ko kun yi laifi kaza bisa ga wannan za mu rusa muku muhallinku babu wannan”.

Ya ce a yanzu matakin da za su ɗauka shi ne na zuwa kotu; “Dokar da suka kafa su suke saɓawa, amma za mu bi ko su aiwatar ko kar su aiwatar, mun yi wannan. Yanzu na farko mu tara ku nan muna son a isar mana da wannan saƙon muna son duniya ta san wannan zaluncin da ta’addancin. Sannan akwai matakai daban-daban. Muna kuma addu’a Allah ta’ala tunda dai wani ya zalunci wani yana ganin yana da ƙarfi, to akwai wani wanda ya fi shi ƙarfi. Akwai kuma matakin zuwa shari’a domin isar da kokenmu”, ya ƙarƙare.


Comments

3 responses to “Muna da ‘yancin mallakar muhalli don gudanar da rayuwarmu – Martanin almajiran Shaikh Zakzaky ga El-Rufai”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Muna da ‘yancin mallakar muhalli don gudanar da rayuwarmu – Martanin almajiran Shaikh Zakzaky ga… […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Muna da ‘yancin mallakar muhalli don gudanar da rayuwarmu – Martanin almajiran Shaikh Zakzaky ga… […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Muna da ‘yancin mallakar muhalli don gudanar da rayuwarmu – Martanin almajiran Shaikh Zakzaky ga… […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *