No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jam’iyyar APC a Kano sun ce sun rungumi ƙaddara game da hukuncin kotun ƙolin Najeriya da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Sakataren jam’iyyar na jiha Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida wa BBC cewa sun karɓi ƙaddara, suna kuma fatan hakan ya zame musu alheri.

Ya ce kuma suna kyautata wa Allah zato cewa tabbas hakan zai zama alheri a gare su.

”A yanzu muna cikin alhini, kuma bai kamata mu ɗauki mataki a lokacin alhini ba, amma idan ƙura ta lafa, za mu zo mu zauna, mu shirya domin tunkarar zaɓen 2027”.

Tun da farko dai jam’iyyar ce ta yi nasara a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara, kafin yau kotun ƙoli ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan farkon.

KU KUMA KARANTA: Saƙon Gwamnan Kano Abba Kabir Ga Nasiru Yusuf Gawuna

”Allah ya sa hakan ne ya fi alheri, kuma muna bai wa ‘yan jam’iyar mu na APC da sauran al’ummar jihar kano haƙuri, tare da ƙiran a zauna lafiya”, in ji shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...