Asusun tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da ƙungiyar lafiya ta Gavi, sun fitar da sanarwar cewa nan ba da jimawa ba, za a kawo ƙarshen cutar zazzabin cizon sauraro, musamman a wasu ƙasashen Afirka da cutar tafi ƙamari, ta hanyar rarraba alluran rigakafin wannan cuta da ke yiwa ƙananan yara kisan mummuke.
Wannan na zuwa ne, bayan jirgin farko ɗauke da dubban alluran wannan rigakafi da ya sauka a Jamhuriyar Kamaru, bayan da aka gudanar da gwaje-gwajen rigakafin cutar a ƙasashen Kenya, Ghana da Malawi, har ma aka samu nasarar rage adadin masu kamuwa da ita fiye da yanda aka tsammata.
Hukumomin lafiyar biyu sun bayyana wannan ci gaba na allura da aka samu a matsayin, musamman wajen kawar da ɗaya daga cikin cutuka mafiya hatsari da ke barazana ga ƙananan yara a nahiyar Afirka.
KU KUMA KARANTA: Binciken Jami’ar Oxford ya tabbatar allurar riga-kafin zazzaɓin cizon sauro data ƙirƙira na bada kariya, na tsawon shekara biyu
Karin masu alluran rigakafin da adadin su ya haura miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai, nan ba da jimawa ba UNICEF ya ce za a aika su kasashen Burkina Fasio, Laberiya, Niger da kuma Saliyo.
Shugaban UNICEf, Catherine Russell, gabatar da wannan shiri na rigakafi, shakka babu zai kawo ƙarshen fargabar da iyaye da kuma hukumomin lafiya ke ciki, game da illar da wannan cuta ke haifarwa a ƙasashe, musamman masu raunin tattalin arziki.
Ƙasashen Afirka da dama na shirye-shiryen yadda za su sanya alluran rigakafin zazzabin cizon sauro cikin rukunan rigakafin da ake yiwa yawa, inda ake sa ran za su fara amfani da wannan shiri daga Watan Janairu zuwa Maris ɗin shekarar baɗi.