Mun kammala kai hare-haren da muka tsara kaiwa Iran – Isra’ila
Isra’ila ta ce, ta kammala wani gagarumin hari akan Iran bayan sama da shekara guda da aka kwashe ana ba ta kashi, da ya samo asali da wani hari da dakarun Hamas da Iran ke marawa baya suka kai kan ƙasar Isra’ila, da ya rikiɗe zuwa wani rikicin da kai tsaye yake gudana da Iran da Hizbullah a yankin.
Cikin wata sanarwa da aka fitar da safiyar ranar Asabar, Rundunar mayaƙan Isra’ila ta ce, jiragen yaƙin ta sun koma gida lami lafiya, bayan kai wani tsararren harin soji a wurare da dama a Iran. Ta fitar da sanarwar ne kimanin sa’oi 4 bayan samun rahoton farko da ya ɓulla na wata fashewa a Iran da kimanin karfe 2:30 na asuba a birnin Tehran.
Rundunar dakarun tsaron Isra’ilan ta ƙara da cewa, bisa rahotannin sirrin da ta samu, dakarun saman ta, sun kai hari kan masana’antar Ƙera makamai masu linzami da ake amfani da ita wajen ƙera makamai masu linzamin da Iran ta riƙa harbawa cikin Isra’ila a shekara gudan da ta wuce. Rundunar ta ce, waɗannan makamai masu linzami nayin barazana kai tsaye ga al’ummar Isra’ila.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa, jamhuriyar Musulunci ta Iran ɗin ce ta kakkaɓe dukkan hare-haren da Isra’ila ta kai a birnin Tehran da ke Iran.
Haka zalika, rundunar dakarun tsaron ta kai wani hari ta sama da ta ƙasa kan wasu muhimman wurare a Iran, da nufin karya lagon irin hare haren da Iran ɗin ke kaiwa Isra’ila.
Mai Magana da yawun rundunar, Rear Admiral Daniel Hagari ya shaidawa manema labarai cewa, Isra’ila ta yi nasara a hare haren ta sama da ta gudanar, duk da dai anan take ba ta gabatar da wata sheda akan iƙirarin nata ba.
KU KUMA KARANTA:Sojojin Isra’ila sun ce, ba za su ci gaba da yaƙi ba, idan har…
Shafin kafar labarum Iran IRNA ta jiyo hukumar tsaron sararin saman ƙasar na cewa, Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin soji a birnin Tehran da yankin arewacin Khuzestan da Ilam. Ta ƙara da cewa, dakarun na Iran sun yi nasarar daƙile hare haren, su ka tabbatar da cewa, ɓarnar da harin ya haifar ba ta da yawa.
Mataimakin shugaban Iran na farko Mohammad Reza Aref ne kaɗai babban jami’i da ya tofa albarkacin bakin shi akan hare haren na Isra’ila na safiyar Asabar. Ya wallafar tutar kasar musuluncin a shafin sadarwar zamani na X inda ya rubuta cewa’ Shugabannin Iran sun tozarta makiya kasar mu ta haihuwa.’
Hukumomin na Iran basu gabatar da wata shedar da ta nuna cewa sun dakile hare haren da Isra’ilan ta kai mata ta sama ba, ko cewa ba wata barna da ta abku. To sai dai kafar yada labarum kasar ta sanar da jiyo dakarun Iran na cewa, harin na Isra’ila ya hallaka sojoji biyu.
Wani babban jami’in Amurka ya shaidawa manema labarai cewa, Isra’ila ta kai tsararrun hare hare ta sama kan wuraren soji dabam dabam a sassan Iran da wajen wuraren dake da yawan mutane.