Ministocin tsaro da muhalli na ƙasar Ghana sun rasu a hatsarin jirgin sama
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin kasar Ghana ta tabbatar da rasuwar ministan tsaron kasar Edward Omane Boamah da ministan muhalli Alhaji Murtala Muhammed sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu mallakin rundunar sojojin sama ta kasar Ghana.
Sauran wadanda suka rasu sun hada da mataimakin shugaban jam’iyyar NDC Samuel Sarpong da tsohon dan takarar majalisar tarayya Samuel Aboagye, da kuma ma’aikatan jirgin.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin jirgin sama ya yi sanadiyar mutuwar mutum 18
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya tashi daga birnin Accra zuwa yankin Obuasi, inda yayi hatsari akan hanya.
Kawo yanzu ba a kai ga tabbatar da dalilin hatsarin jirgin ba.









