Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, a cewar wasu majiyoyi na diflomasiyyar Turkiyya.
Fidan and Haniyeh sun tattauna ranar Asabar kan batun tsagaita wuta nan-take a Gaza da kai ƙarin kayan agaji yankin da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da ƙasashe biyu masu ‘yancin kansu.
Hare-haren da Isra’ila take kai wa a Gaza sun raba kashi 85 na mutanen yankin da muhallansu a yayin da ake cikin tsananin rashin abinci da ruwa mai tsafta da magunguna, sannan an rusa kashi 60 na gine-ginen yankin, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
A watan Oktoban da ya wuce, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Haniyeh bayan Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza inda ya tabbatar masa cewa Ankara zai kai kayan agaji Gaza sannan za a ɗauko waɗanda suka jikkata a yankin domin kawo su Turkiyya su yi jinya idan akwai buƙatar hakan.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis
Shugaba Erdogan ya jaddada cewa ba za a samu dauwamammen zaman lafiya a yankin ba sai Falasɗinawa sun samu kasa mai zaman kanta kamar yadda take a 1967 wacce Birnin Kudus zai zama babban birninta.
Erdogan ya ƙara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da fafutuka domin ganin an samu zaman lafiya a yankin.
Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare babu kakkautawa ta sama da ta ƙasa a Gaza tun bayan da Hamas ta kai mata barin ba-zata, wanda Tel Aviv ya ce ya kashe aƙalla mutum 1,200.
Ta kashe Falasɗinawa aƙalla 24,927, galibinsu mata da ƙananan yara, sannan an jikkata mutum 62,388, a cewar hukumar lafiya ta Falasɗinu.