Isra’ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis

0
120

Isra’ila ta kashe farar hula aƙalla bakwai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza da kuma unguwar Al Amal da ke Khan Younis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito.

Jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari wani gida mallakar iyalan Darwish a sansanin, wanda hakan ya jawo kisan farar hula biyar a sansanin da kuma raunata wasu da dama.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa sama da 60 a cikin dare ɗaya

Haka kuma jiragen yaƙin na Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare da dama a unguwar Al Amal inda suka kashe aƙalla mutum biyu da kuma raunata wasu da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here