Ministan da zai wakilci jihar Kaduna, ya faɗi a wajen tantancewa a zauren majalisa

0
297

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ɗaya daga cikin ministocin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura wa Majalisar dokokin ƙasar domin tantancewa ya yanke jiki ya faɗi a zauren majalisar.

Ministan wanda ya fito daga jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal ya faɗi ne a daidai lokacin da ya kammala jawabi kan tarihin rayuwa da karatunsa.

Sai dai nan da nan aka ɗaga shi kuma aka zaunar da shi a kan kujera.

Majalisar dai ta shiga zaman sirri bayan faɗuwar sa.

Tun farko a lokacin da yake jawabi, Abbas ya shaida wa majalisar cewa ya yi matuƙar murnar damar da ya samu, kuma yanayi ne da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba.

Leave a Reply