Daga Maryam Umar Abdullahi
Mai martaba Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Yamusa III, ya ce mayar wa sarakunan gargajiya waɗansu ikon su na ɗaya daga inda za’a samu nasarar yaƙi da matsalolin tsaro.
A yayin da wasu masana tsaro ke matsin lamba ga gwamnati Najeriya a kan ta ɗauki yaƙi da matsalolin tsaro musamman a arewacin ƙasar da muhimmanci, masu ruwa da tsaki da suka haɗa da babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya, Gwamnonin Arewa maso yamma, kama daga Dauda Lawal na jihar Zamfara, Dikko Raɗɗa na jihar Katsina, Uba Sani na jihar Kaduna, Bala Muhammad na jihar Bauchi da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya, sarakunan gargajiya da dai sauransu, sun lashi takobin kawo ƙarshen matsalolin tsaro a arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya ta hanyar al’umma tare da cewa haɗa gwiwa daga ɓangaren tarayya zuwa jiha shi ne mafita.
Da ya ke bayani a taron, ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya jaddada muhimmancin haɗa gwiwa wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.
Alƙawura daga bakin waɗannan masu ruwa da tsakin dai na zuwa ne jim kaɗan bayan buɗe taron yini biyu na nazari a kan matsalolin tsaro da zimmar kawo mafita mai ɗorewa da gamayyar ƙungiyoyin Arewa wato ‘Coalition of Northern Groups’ (CNG) da ta fara a yau Laraba, inda aka tafka muhawara mai ƙarfi a kan sakamakon binciken ƙungiyar ta CNG don warware matsalolin waɗanda suka ƙara ƙamari a makonnin baya-bayan nan.
Alhaji Nastura Ashir Shariff shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu ƙungiyar CNG wadda ya bayyana cewa a ƙungiyance, sun fitar da wata manhaja da za ta kula da yadda za’a yi amfani da gudumuwar al’umma gabaɗaya don kawo ƙarshen matsalolin tare da taimakawa al’ummar da matsalolin tsaro ta kassara su.
A wani ɓangare kuwa gwamna Dikko Raɗɗa na jihar Katsina, wanda shi ya fara kafa wata rundunar tsaro na musamman don taimakawa asalin rundunonin tsaron Najeriya yace, haɗin gwiwar da ake gani tsakanin gwamnonin arewa maso yamma abu ne mai ƙarfafa gwiwa a yaƙi da matsalar tsaro.
Shi ma takwararsa na jihar Zamfara, Dauda Lawal, cewa ya yi tattaunawa tsakanin gwamnonin arewa maso yamma da sauran masu ruwa da tsaki da kuma fitar da siyasa wajen yaƙar lamarin su ne kashin baya ga murƙushe matsalolin tsaro a arewacin Najeriya.
Sanata Uba Sani da shi ne gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana cewa, ba wata jiha ɗaya da za ta iya magance matsalolin tsaro ita kaɗai, sai an haɗa gwiwa baya ga cewa an duba yadda za’a kawo ƙarshen matsaloli masu alaƙa da tattalin arziƙi.
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
hakazalika, Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi wanda a cewarsa ba za’a kawo gyara a matsalolin tsaro ba ba tare da gwamnoni ba kuma rashin sanya idanu daga ɓangaren gwamnonin ma na ƙara yin tarnaƙi ga samun nasara a kan matsalolin.
KU KUMA KARANTA: Iran ta ce a shirye take ta taimakawa jamhuriyar Nijar, don shawo kan takunkuman da aka ƙaƙaba mata
Ya ƙara da cewa sa ido akan komai a gwamnatance shi ne babban dabara.
Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta wato INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya buƙaci dukkan masu faɗa a ji a arewa da ma Najeriya baki ɗaya su guji barin bambancin siyasa ya zama matsala wurin haɗa kai domin a magance matsalolin tsaro.
Haka kuma, Mai Martaba, Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Yamusa III, ya ce mayarwa sarakunan gargajiya waɗansu ikonsu na daya daga inda za’a sami nasara a yaƙi da matsalolin tsaro.
A ɓangare guda kuma Babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce matsalar da aka samu ba’a ɗauki mataki da wuri a kan matsalolin tsaro ba yana mai cewa dukkan ɓangarorin tsaro a ƙasar za su haɗa gwiwa wajen magance matsalolin kuma suna buƙatar gudumuwar al’umma wajen samun nasara
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Abdulsalam Abubakar, ya yi fatan cewa a ƙarshen taron na CNG, za’a sami shawarwari ga gwamnatin kan aiwatar da mafita ga matsalolin tsaron Najeriya.
A maganar yaƙi da ‘yan ta’adda masu sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, masana tsaro dai na ƙara jaddada muhimmancin a yi amfani da bayanan banki da na lambar shedar zama ɗan ƙasa na NIN dake haɗe da layukan sadarwa da wasu ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen karɓar kuɗin fansa don magance wannan matsalar.