Mawaƙi Ali Jita, ya fice daga jam’iyar NNPP zuwa APC

0
95
Mawaƙi Ali Jita, ya fice daga jam'iyar NNPP zuwa APC

Mawaƙi Ali Jita, ya fice daga jam’iyar NNPP zuwa APC

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mawaƙi Ali Jita ya cire jar hula ya fice daga NNPP Kwankwasiyya zuwa APC ta hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Ibrahim Jibrin Maliya.

Jita dai yana cikin jiga-jigan ‘yan Kwankwasiyya daga masana’antar fina-finan Hausa, shi ne ya yi fitacciyar waƙar nan ta ‘Abba Gida-gida Abba ne…’.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Sanata Barau ke ci gaba da yiwa ‘yan Kwankwasiyya tsamen nama.

Ko a kwanakin baya ma Sharu Habu Tabule da Rabi’u Daushe sun fice daga Kwankwasiyyar zuwa APC gidan Barau.

KU KUMA KARANTA: Wata kotu a Kano ta bayar da belin ɗan jarida kan sukar gwamnatin jihar 

A gefe guda kuma ana ta samun masu kokawa da tsarin da ‘yan Kannywood na Kwankwasiyya ke ciki, kamar su Jarumi Garzali Miko da Jaruma Hafsat Muhammad da Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya fina-finai ta Ƙasa Malam Salisu Officer sun fito sun koka.

Ko me ke jawo hakan?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here