No menu items!

Sample Page Title

Date:

Matatar Ɗangote za ta rarrarba Man Fetur kai-tsaye zuwa gidajen Mai

Daga Jameel Lawan Yakasai

Matatar Dangote ta sanar da cewa zata fara rarraba man fetur (PMS) da dizal a duk faɗin Nijeriya tun daga ranar 15 ga Agusta, 2025.

Wannan shiri zai baiwa masu sayarwa, da ‘yan kasuwa, da masana’antu da sauran manyan masu amfani damar sayen Man kai tsaye daga kamfanin.

KU KUMA KARANTA: Dangote ya yi ritaya a matsayin shugaban kamfanin sa

Don inganta hanyoyin rarrabawar Matatar ta ƙaddamar da sabbin tankokin iskar gas (CNG) guda 4,000 da kuma gina tashoshin samar da iskar ta CNG.

Wannan tsarin zai rage farashin sufuri da kuma taimakawa wajen rage farashin kayayyaki masu amfani da man fetur.

Sanarwar ta nuna cewa wannan shiri ya yi daidai da shirin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Tinubu. An buƙaci masu sha’awar shiga wannan shirin su yi rijista tsakanin ranar 16 ga Yuni zuwa 15 ga Agusta.

Matatar ta ce, wannan shiri na daga cikin ƙoƙarinsa na taimakawa wajen samar da man fetur mai arha a Nijeriya, wanda zai inganta rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...