Yawan cin Kaza na haifar da kansar hanji – Bincike
Daga Jameel Lawan Yakasai
Wani sabon bincike ya nuna cewa cin kaji har sau huɗu a rana na iya ninka haɗarin kamuwa ko mutuwa daga wasu cututtukan daji na hanji.
Duk da cewa an daɗe ana danganta jan nama mai da ƙarin haɗarin cutar daji, an dade ana ɗaukar kaji a matsayin zaɓi mafi aminci — sai dai yanzu abubuwa sun canza.
Masu bincike daga ƙasar Italiya sun nazarci halayen cin abinci da tobayanan lafiya na kusan mutane 5,000, mafi yawancinsu a cikin shekarunsu na 50, cikin fiye da shekaru ashirin.
KU KUMA KARANTA: Cutar Lassa: Gwamnatin Kano za ta kashe Ɓerayen ƙaramar hukumar Garun Malam
Sun gano cewa mutanen da ke cin fiye da gram 300 na kaji a kowane mako — daidai da kusan rabo huɗu — suna fuskantar haɗarin mutuwa daga cututtukan daji na hanji sau biyu fiye da waɗanda ke cin kasa da rabo ɗaya a mako.
Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar Nutrients, ya tabbatar da cewa wannan haɗari yana da alaƙa da cututtukan daji na ciki, hanji, hanta, ƙoda da sauran sassan narkar da abinci.
Cin fiye da rabo huɗu na kaji a mako ana danganta shi da ƙarin haɗarin mutuwa daga kowanne irin dalili da kashi 27 cikin 100. Maza sun fi fuskantar haɗarin, duk da cewa ba a bayyana dalilin hakan ba a fili.
Masana sun bayyana cewa iya bambancin sinadaran hormone tsakanin maza da mata na iya taka rawa, ko kuma saboda maza na cin abinci da yawa fiye da mata, wanda ke ƙara haɗarin kamuwa.
Daga cikin dalilan da ake zargi da haifar da haɗarin sun haɗa da samuwar sinadarai masu guba yayin da ake dafa kaji da zafi mai yawa, amfani da ƙarin abinci (feed additives), ko magungunan da ake amfani da su a gonakin kaji. Masu binciken sun amince da cewa bincikensu ba ya da cikakken bayani, musamman game da yadda ake dafa abincin da kuma yawan motsa jiki.