Matashi ya ƙirƙiri na’urar hana direbobi barci a yayin tuƙi a Jihar Kano

0
244
Matashi ya ƙirƙiri na’urar hana direbobi barci a yayin tuƙi a Jihar Kano

Matashi ya ƙirƙiri na’urar hana direbobi barci a yayin tuƙi a Jihar Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Wani matashi me suna Ibrahim Bala, ɗan asalin ƙaramar hukumar Bichi dake Kano, ya ƙirƙiro na’urar da zata riƙa hana Direbobi barci a yayin da suke tsaka da tuƙi wato “Driver’s Anti Sleep Alarm Device”.

Matashin me kimanin shekaru 22 a duniya ya samar da na’urar ne wadda za ta ringa ankarar da Direbobi, Idan barci yana ƙoƙarin ɗaukar su a lokacin da suke tsaka da tuƙi.

KU KUMA KARANTA:Dokace ta bawa hukumar tace fina-finai damar tace kowanne nau’in Bidiyo – Isma’ila Afakallah

Da yake zantawa da yake zantawa d Manema labarai Matashi Ibrahim Bala, ya ce wannan babban ci gaba ne da zai taimaka matuƙa, musamman wajen rage afkuwar haɗɗura a hanyoyi, a tsakanin Direbobin ƙananan da manyan motoci a sakamakon fuskantar gajiya a lokacin tafiye-tafiye.

Ya kara da cewa wannan fasaha dama sauran fasahohin da matasan yankin arewa suke samar wa za su taimaka sosai la’akari da yadda ake yawan samun masu ƙirƙirar abubuwa da dama, adan haka akwai buƙatar a dinga basu kulawa ta musamman ta fuskar ƙarfafa musu guiwa akan tarin baiwar da Ubangiji ya yi musu.

A ƙarshe ya yi fatan mahuntan yankin arewa, musamman shugabannin siyasa, ‘yan kasuwa, masu kudi dama sauran masu ruwa da tsaki za su dinga taimaka wa matasa irin su masu fasaha, domin samun damar cika mafarkansu.

Ana yawan samun ƙananan yara da matasa a arewacin Najeriya masu ɗauke da baiwa kala daban-daban, ta yadda suke ƙirƙirar abubuwan da ake amfani da su a kasar wadanda kuma shigowa ake da su, ko kuma wasu abubuwan da a tarihin ƙirƙire-ƙirƙire ma ba’a taba samar da irinsu ba.

Leave a Reply