Dokace ta bawa hukumar tace fina-finai damar tace kowanne nau’in Bidiyo – Isma’ila Afakallah

0
52
Dokace ta bawa hukumar tace fina-finai damar tace kowanne nau'in Bidiyo - Isma'ila Afakallah

Dokace ta bawa hukumar tace fina-finai damar tace kowanne nau’in Bidiyo – Isma’ila Afakallah

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Tsohon Shugaban Hukumar tace fina-finan da dab’i ta Jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah ya magantu, kan yadda ake Cece – kuce akan tsare – tsaren da Hukumar tace fina-finan keyi, karkashin jagorancin Abba El-Mustapha.

Wanda Afakallah yace hukumar nada damar yin hukunci ga duk wanda ya karya dokar hukumar, kuma hukumar nada hakki tayi doka akan dukkan bidiyon da aka fitar ko a wacce kafa ce.

KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai ta kara soke lasisin wasu gidajen wasannin gala 8 tare da Haramta aikinsu na din-din-din a Jahar Kano

Afakallahu ya kuma ce, tabbas dole a yabawa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya kafa hukumar tace finafinai da dab’i ta Jihar Kano a zangon mulkinsa na farko (1999 – 2003), wacce har yanzu take taka rawa wajen tafiyar da harkokin nishadi don ganin ba’a sabawa addini ko al’ada ba.

Ya kuma ce, yaso ace a shugabancinsa aka yiwa dokar hukumar gyara, amma dukda haka yana goyon bayan matakan da hukumar ke dauka a yanzu, illa iyaka wasu ‘yan kura-kurai da yake fatan hukumar zata gyara.

Leave a Reply