Wasu masu gasar ’yar-ƙuren shan miyagun ƙwayoyi a bikin ɗaurin aure a jihar Katsina sun faɗa hannun hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi (NDLEA).
Mutum 25 ne jami’an NDLEA suka cafke a yayin da suke tsaka da gasar shan miyagun ƙwayoyin a wani shagalin kafin ɗaurin aure a unguwar Shola a Katsina.
Kakakin NDLEA Femi Babafemi ya ce a yayin samamen da aka cafke mutanen, an same su da ƙwayoyi da suke cakuɗawa a cikin wani bokiti suna sha.
“Duk da cewa angon da ya shirya gasar shan miyagun ƙwayoyi tare da abokansa ba ya wurin a lokacin, daga baya mun kamo shi,” in ji Babafemi.
Ya ce hukumar ta kama wani ɗan shekara 29 a Abuja ɗauke da tramadol ƙwaya 49,000 da alluran pentacozin 6,000, waɗanda ya ce zai kai wa masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne a yankin Doguwa a Jihar Kano.
A Jihar Borno kuma an kama wasu matasa uku da ƙwayar tramadol 81,975, biyu daga cikinsu a jihar, na ukun kuma sojoji suka kama shi a garin Mubi, Jihar Adamawa.
Hukumar ta kuma wata mace da maza biyu, har da ɗan ƙasar Jamhuriyar Nijar a wurare daban-daban a Jihar Kaduna ɗauke tabar wiwi mai nauyin kilo 81.