Masana kimiyya na Turkiyya sun gano wata ƙwayar halitta da ke jawo ciwon ƙoda ga yara

0
233

Masana kimiyya na ƙasar Turkiyya sun gano wata ƙawayar halitta wadda ke taka muhimmiyar rawa wurin jawo tsananin ciwon ƙoda a yara, wanda hakan ya taimaka wurin bayar da gudunmawa ta ɓangaren ilimin kiwon lafiya na duniya a karon farko.

Dakta Fatih Ozaltin, wanda mamba ne a tsangayar koyar nazarin cututtukan da suka shafi ƙoda da mafitsara a Jami’ar Hacettepe da ke Turkiyya, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an soma binciken kimiyya kan ƙwayar halittar ta FOXD2 a 2021 inda suka yi binciken haɗin gwiwa tare da Sashen Nazarin Kiwon Lafiya na Jami’ar Santambul.

Ozaltin ya bayyana cewa akwai wasu yara ƴan gida ɗaya waɗanda aka haifa da matsala ta ƙoda da mafitsara, lamarin da aka yi bincikensa a Sashen Nazarin Kiwon Lafiya na Cerrahpasa.

Ya bayyana cewa an haifi yaran da cutar ne bayan an yi auren zumunci tsakanin iyayensu, wanda hakan ya jawo aka soma bincike kan ƙwayoyin halitta a danginsu.

KU KUMA KARANTA: Yaƙi tsakanin Isra’ila da Falasɗinu, Rasha da Ukraine ya shafi tallafin kuɗin kiwon lafiya a Afirka – UNICEF

Ozaltin ya bayyana cewa an gudanar da bincike kan lamarin mai taken, “Bincike kan sabbin ƙwayoyin halitta a cutar ƙoda wadda aka gada,” inda aka yi binciken a Jami’ar Hacettepe.

“Bincikenmu na kimiyya ya kai mu ga ƙwayar halittar FOXD2. Mun ƙara mayar da hankali kan yadda sauyi a wannan ƙwayar halittar kan jawo matsalolin da ke tattare da ƙoda

Ozaltin ya yi ƙarin haske game da haɗin gwiwar kasa da kasa bayan Jami’ar Munich ta gano wani dangi ɗauke da irin ƙwayar halittar da ke sauyawa.

“Ta hanyar haɗin gwiwa a bincikenmu, binciken ya nuna cewa ƙwayar halittar FOXD2 na taka muhimmiyar rawa wurin ‘kula da ƙodar ɗan tayi da kuma tafiyar da mafitsara,” in ji shi. “Mun gano cewa sakamakon dabbobi ba su da wannan ƙwayar halittar ta FOXD2, akwai irin waɗannan matsalolin na ƙoda da ke tasowa irin na bil’adama.

Ozaltin ya jaddada cewa an wallafa cikakken sakamakon bincike na wucin-gadi da aka gudanar, lura da cewa masana daga Isra’ila sun ba da rahoton irin wannan lamari a tattare da marasa lafiya.

“Mun gano sauye-sauye irin daban-daban a ƙwayar halitta iri ɗaya a dangi uku dangane da wannan cuta a duniya. Wannan binciken ya zama ɗaya daga cikin hujjojin da ke nuni da cewa wannan matsalar ta ƙwayar halittar FOXD2 ita ce ke jawo irin wannan cuta ta ƙoda a yara.

“A baya an san dangantakar da ke tsakanin sauyi a ƙwayar halittar FOXD2, sai dai ba a san me take haifarwa ba, sai dai a karon farko a duniya an tabbatar da cewa cutar ƙoda na daga cikin abin da take haifarwa,” in ji shi.

Leave a Reply