Martani ga Farfesa Mansur Sakkwato, Daga Mahfuz Mundadu

0
129
Martani ga Farfesa Mansur Sakkwato, Daga Mahfuz Mundadu
Farfesa Mansur Sakkwato

Martani ga Farfesa Mansur Sakkwato, Ra’ayin Mahfuz Mundadu

Idan kana karanta wannan, Farfesa Mansur, ba don kana shirye ka saurara ba ne, sai dai domin gaskiya, kamar gurnani a tsakiyar hudubarka, ta ƙi jiran izinin ka. Mun san yana da zafi. Mun san yana ƙona zuciya. Ba don an kayar da kai ba, amma domin gidan da ka gina da tabbatattun maganganun aro yanzu yana rushewa, ba saboda makaman Iran ba, sai dai saboda matsin lambar sabanin da ke cikinka. Gidan da kake bauta wa ya fara fashewa. Ba kawai fadar Riyadh ba, har da gidan ilimin da ka gina da tubalin Wahhabiyya da simintin Sahayoniyya.

Ka fada mana, Farfesan ƙwarai, wa ya koya maka ƙiyayya haka? Wa ya nada ka mufti na inganci, mai kuma ƙwace wa shahidai Musuluncinsu saboda ba sa durƙusawa ga gumakan Amurka da kake bautawa? Shin ba abin mamaki ba ne cewa ba ka ganin komai na Musulunci a wadanda ke mutuwa suna yaƙar Sahayoniyya, amma kana ganin komai na Musulunci a wadanda ke shan giya da cin abinci a Davos da Tel Aviv? Ka tsani Iran don ta doke Isra’ila, ba don hakan ba daidai ba ne, sai dai don ta yi shi ba tare da izinin ka ba.

To, bari mu ci gaba bisa taka tsantsan, amma ba tare da neman afuwa ba.

KU KUMA KARANTA: Farfesa ya koma siyar da kayan miya saboda taɓarɓarewar tattalin arziki

“Idan munafukai sun zo wurinka, [ya Muhammad], suna cewa, ‘Mun shaida kai Manzon Allah ne.’ Allah kuwa ya san kai Manzonsa ne, kuma Allah na shaida cewa munafukai makaryata ne.” (Alkur’ani 63:1)

Mu fara, kamar yadda Socrates ke so, da tambayoyi. Gaskiya tana bayyana sosai a cikin tambaya fiye da fushi.

Farfesa Mansur, ka ce Iran ba Musulunci take bi ba. Bari mu bincika.

Yaushe ne ka ga Musulunci a cikin bom din Saudiyya da ke fadowa kan asibitocin Yemen? Yaushe ne ka gano Musulunci a cikin musabaha tsakanin Bin Salman da Trump? Yaushe Musulunci ya zama riga da ake dinka a Washington a sa a Riyadh?

Ka ga Iran na yakar zalunci, amma maimakon ka ce “Alhamdulillah,” sai ka ce “Ha wusu bilai.” Shin kompas dinka ne ya baci, ko lamirinka?

Kana ikirarin kana son Ahlul Bayt. Amma idan mabiyansu ‘yan Shi’a an kashe su, sai ka dinga kokawa da sabanin akida maimakon ka nuna Allah wadai. Idan Iran ta tura taimako zuwa Falasdinu, kai kuwa sai ka tura bayanan suka. Idan sun rama kisan Mossad, kai sai ka buya a bayan sharuɗɗa. Ka fada mana, a wane lokaci ne akida ke zama cin amana?

Bari mu kawo Ayatollah Baqir al-Sadr, wanda zurfin iliminsa ke hud karfe, kuma jininsa aka zubar da takobin Ba’athawa da ke kyalli a bukukuwan Saudiyya yanzu.

“Ma’aunin Musulunci na gaskiya shi ne yadda mutum ke tare da wadanda aka zalunta, ba yadda yake iya kawo hadisi yayin cin abincin dare da azzalumai ba.” – Baqir al-Sadr

Abin da Iran ta yi ba tsintsar dabaru ne kawai ba. Ruhaniya ce. Ashura ce da aka jaddada da ‘drones’. Karbala ce da aka sake haihuwar ta makaman zamani. Abin da ke tsoratar da kai, Farfesa, ba jinjirin watan Shi’a ba ce. Abin tsoron ka shi ne, wannan jinjirin watan ya dushe hasken ranarku ta akidar takfir.

Kana cewa Iran ba Musulunci ba ce saboda Shi’a ce. To, idan haka ne, mu ce Saudiyya ba Musulunci ba ce saboda ta ci amanar Gaza, ta yi musabaha da Sahayoniyyawa, ta binne Yemen da duwatsun rushe-rushe? Mu kira ‘yan uwanka Wahhabiyawa kafirai saboda suna durkusa wa kowane jakadan Amurka kamar mage a gaban madarar da ta zube?

Ka dai ga yadda Iran ta jure wa takunkumi, hare-haren yanar gizo, kisan gilla, harin jiragen sama da yakin farfaganda, ta kuma yi nasara. Ka ga yadda ta doke da girgiza daular da ta fi girman kai a zamaninmu. Amma a cikin dukkan jawabinka, ba ka taba yin Allah wadai da masu zalunci ba — ko sau daya ma. Maimakon haka, ka zargi masu nasara da laifin samun nasara ba tare da izinin akidar ka ba.

Bari in fada maka gaskiya, Farfesa: Wannan ba sabanin fikihu bane. Ba ma bambancin Sunni da Shi’a bane. Wannan tsohon yaki ne na rai — tsakanin masu goyon bayan Ali da masu cin abinci tare da Yazid.

Idan bijire wa zalunci ba Musulunci bane, to menene Musulunci? Idan taimaka wa Falasdinu, Siriya, Labanon, Iraki da Yemen ba Musulunci bane, to me ya rage daga Musulunci — ibada da riya kawai? Kana son Musulunci mai sawa a yi shiru, wanda ba zai katse hirar mulkin-mallaka ba. Amma ka sani wannan Musulunci yana da ɗaga murya, yana kwarmato kamar Zaynab a kotun Yazid, yana sadaukar da jini kamar Husain a filin Karbala.

Ga abin da Rumi ya ce:
> “An haife ka da fikafikai, me yasa kake son yin rarrafe a rayuwa?”

Iran ta riga ta tashi sama, kai kuma kana rarrafe. Ka shagaltu da yawa wajen tsotsan takalmin malamai masu kuɗin fetur har ba ka lura cewa Ahlul Kisa sun tashi — ba da takobi ba, sai dai da ‘drones’, makamai masu saurin gaya wa jini na wuce tare da karfin guiwa.

Ka ce babu wani Musulunci da ya yi saura a Iran, amma ka ce Saudiyya cike take da Musulunci. Saudiyyar fa da ta kashe dan jarida a ofishin jakadanci. Ita ce fa Saudiyyar da ta killace Qatar don ba ta goyi bayan Sahayoniyyawa ba. Saudiyyar fa da ta gina otal ga Malaman Yahudu Sahayoniyyawa a Madina, kuma tana hana Musulmi su yi juyayi na Ashura a Riyadh.

To, yanzu mu bude Alkur’ani don mu ga wa ke kama da Ashabul Kahfi (Sahabban Kogo), kuma wa ke kama da masu gina dan marakin zinariya?

Haƙika Iran tana da kura-kurai. Amma kura-kuranta na mai kokarin bin gaskiya ne, ba na mai cin amana ba. Kurakuranta na kasa ce da ke tafiya a kan igiyar kaddara, ba wacce ke kwance da bargo na Sahayoniyya ba. Ita tana gina asibitoci da jami’o’i a cikin kunci, alhali abokan aikinka suna gina fadodi da gidajen caca a karkashin sunan Allah.

Mu koma Karbala. A daren goma na Muharram, Imam Husain ya kashe fitilu, ya ce wa sahabbansa su ‘yanta kansu su tafi. Da yawa sun tafi. Wadanda suka tsaya kuwa sun zama taurarin da ke jagorantar masu neman ‘yanci har abada. Iran a wannan zamani ta zama daya daga cikin wadannan taurari. Kai kuma, Farfesa, kana korafi kan haskenta.

Ya Farfesa, ta yaya ba ka ganin wannan a matsayin Ashura ce aka maimaita? Lokacin da sojojin Yazid suka kewaye Husain, sun yi kama da kawancen da Iran ta fuskanta; Sahayoniyyawa, kabilanci, mulkin-mallaka da rufa-rufa na malamai. Husain ya tsaya ba don zai ci yaki ba, sai don ya riga ya ci nasara ta tsayawa kan gaskiya. To Iran ta ci duka biyun ne.

Ba Iran ce matsalarka ba. Matsalarka gaskiya ce da ta ki tuntubar ka.

A yakin Ahzab, Alƙur’ani ya ce:
“Ga shi! Sun zo muku daga sama da kasa… idanunku sun bude, zukatanku sun kai makogwaro…” (33:10)
Amma mumini ya ce:
“Wannan ne Allah da Manzonsa suka yi mana alkawari.” (33:22)

Iran ita ce wannan mumini. Ta tsaya, an kewaye ta. Zuciyarta ba ta karye ba. Ba ta gudu Washington ba. Ta gina makamai ta yi hakuri. Ba ta tambayi Najad fatawa ba. Ta tambayi Alƙur’ani ’ani ƙarfin guiwa.

Kana tambayar: “Me ya sa mutane ke son Iran?” Zan faɗa maka. Ba don ba ta da kura-kurai ba, sai dai don ba ta jin tsoron kowa sai Allah. Shahidanta ana binne su a sahu-sahu, ba a asirce su a asusun banki na waje ba. Ko da ta kuskure, tana kuskure ne a kokari, ba a cin amana ba.

Bari in tunatar da kai daga Nahjul Balagha:
> “Malamin da ya yi shiru a gaban zalunci, to Shaidan ne kurma.” — Imam Ali (AS)

Kai, Farfesa, ba Shaidan kurma bane. Shaidan mai hayaniya ne. Kana magana, amma ba kan zalunci ba; kana magana ne kan masu kiyayya da shi. Kai ne malamin fadar Fir’auna da ke sanye da ɗan kwalin keffiyeh.

Ba ka ce komai ba lokacin da Mossad ta kashe masana kimiyyar Iran. Ka yi dariya lokacin da masu kisan suka dauki bidiyon ta’addancin su. Ka yi ba’a da Iran kan kare kanta, amma ka yaba wa Saudiyya da ke sayar da mai don ɗaukar nauyin sojojin Amurka a yankin. Shirun naka kan Sahayoniyya yana da nauyin gaske. Abin da kake faɗa kan Iran kuma abin takaici ne.

Yanzu dai ƙusurwar masu mukawama (Axis of Resistance) ta bayyana nasara. Kuma martaninka ba “Alhamdulillah” ba ne, sai “Yaya suka iya haka?” Kana so duniya, inda Iran ke rokon yamma. Amma Iran ba ta yin sujada sai ga Allah. Wannan ne ke ɓata maka rai.

> “Rauni shi ne inda haske ke shiga.” — Rumi

Iran ta ji rauni, haske ya shiga. Ba ta hanyar makamai kawai ba, har da shahada, rundunonin Fatemiyoun da Zainabiyoun, marayu da aka raina da ƙarfin gwiwar Husaini, matasan masana da ba su kuka don a ba su iPhones ba sai don Falasdinu.

Kai, Farfesa, kuka kake don a san da kai. Wannan ne dalilin da ya sa kake kai suka ga Iran — ba don ka yi imani ba, sai don rashin tasiri.

Kana cewa Iran ba ƙasar Musulunci ba ce, domin irin Musuluncin da kake so mai yin shiru ne gaban Bani Saud. Kana son Musulunci mai sa hannu a yarjejeniya da masu keta alfarmar Masjidul Aqsa. Amma wannan “Musuluncin” ya mutu. Iran ta binne shi a cikin baraguzan Haifa, Tel Aviv da Ashdod.

Ba mu zo nan don mu sauya maka ra’ayi ba. Mun zo mu fuskance ka ne — da tsoronka, shirunka, munafuncinka, da jahilcinka mai cutar da bil’adama.

Kana iƙirarin kare Sunnah, amma me ya sa kake kawance da masu kashe zuriyar Annabi? Kana cewa kana adawa da Sahayoniya, amma me ya sa kake kai suka ga kasa daya tilo da ke fuskantar ta?

> “Kada ku gauraya gaskiya da ƙarya, ko ku boye gaskiya alhali kuna sane.” (Alƙur’ani 02:42)

Ga gaskiyarka, Farfesa mai sabani: Ka tsani Iran ne don ta yi nasara. Ka ji tsoron Iran don ta tsaya ƙyam. Ka yi isgili da Iran don tana tunatar da kai abin da kake riyawa — Mumini.

Abin da ya fi bayyana, Farfesa Mansur, ba kiyayyar ka ba ce, sai dai yadda ka lullube ta da rigar ilimi. A ce yau Farfesan da aka dora wa nauyin ilimi, amma sai ga shi ya fada cikin ruwan najasar ƙiyayya, hakan ya fi kowace kafa a cikin ilimin da ka ƙirƙira muni. Ba kai kadai ya kamata ka ji kunya ba — har da jami’ar da ta ba ka wannan mukami.

Da can jami’o’i cibiyoyin tunani ne. Yanzu wasu sun zama gidajen karnukan farauta, suna haushi ba kan jahilci ba, sai kan masu bijirewa; ba kan zalunci ba, sai kan akidar da ba ta durkusawa. Idan samun matsayin Farfesa yana nufin maimaita ra’ayin takfiri irin na Riyadh, to duniya ta sani cewa yanzu fa samun karin girma a wasu jami’o’i ba bisa bincike ba ne, sai bisa biyayya ga ra’ayin Wahhabiyawa.

Shin digirin PhD dinka, ka samu ne da bincike ko karanta dokar fada? Ka kare sakamakon bincikenka (thesis) ne ko ka rera taken Saudiyya ta baibai da kyallen “Mutuwa ga Shi’a”? Jawabanka na bainar jama’a sun nuna kai ba Farfesa na Musulunci ba ne — sai dai ma’aikacin mummunan laifin nan na Sahayoniyya.

Jami’ar da ta ba ka matsayin Farfesa, ya kamata ta sake duba litattafanta: ko dai ta janye wannan matsayi ta wanke kanta, ko ta bayyana wa duniya cewa wasu jami’o’i sun maye gurbin bincike da lambobin talla na akida: Ka zama Wahhabi, ka samu Digiri kyauta. “Digiri, biyu aahu.”

To, menene darussan da za a koya?
– Takfiri 101: Yadda ake kiran miliyoyin Musulmi murtaddai kafin asuba.
– Nazarin Sahayoniyya mai zurfi: Shiru idan Isra’ila ta kai hari.
– Gudanar da Zalunci: Yadda ake zagin shahidai a yaba wa ‘yan daba.
– Kiyayyar Shi’a: Tsoron Iran a matsayin kundin ƙarshe na kammala karatu.

Idan ilimi haka ya zama… idan an maye gurbin littattafai da shaci-fadi, hujjoji da bauta, ilimi da hayaniya, to a sani: ba muna ganin muhawara ba ne. Muna kallon yadda ake mayar da akidar karen farauta a matsayin ilimi a jami’a.

Amma ba za mu yi shiru ba. Kamar yadda Imam Ali (AS) ya jaddada:
> “Shirunka kan ƙarya ya fi maganarka ƙarfi.”

Bari ya karade dakunan karatu, masallatai, kogon duwatsu da ramukan ƙarƙashin ƙasa na muƙawama:

Rigar Annabi ba ta Malaman fada bace. A jiƙe take da jini, ana sa ta a hamada, ba ta rayuwa da digiri, sai da aiki.

Kuma Iran, abin mamaki da baƙin ciki gare ka, ta sa ta, ta kuma dace da ita.

Leave a Reply