No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga bayan labule da jagororin Majalisar Dattawa a Yammacin wannan Talatar.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya jagoranci tawagar sanatocin da ta kai wa shugaban ƙasar ziyara kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Ganawar dai na zuwa ne sa’o’i bayan da Majalisar Dattawan ta dakatar da Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmed Ningi har na tsawon watanni uku kan sukar da ya yi dangane da Kasafin Kuɗin ƙasar na bana.

Cikin tawagar sanatocin da ta ziyarci Fadar Shugaban Ƙasar har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin.

KU KUMA KARANTA: Majalisa ta dakatar da sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku

Neptune Hausa ta ruwaito cewa, Sanata Ningi wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa kuma Shugaban Kwamitin Kidayar Al’umma na Majalisar Dattawa, ya yi murabus daga duk muƙaman bayan hukuncin da aka ɗauka a kansa.

An dai dakatar da Sanata Abdul Ningi a ranar Talata, bisa zargin da ya yi na cewa an yi cushe naira tiriliyan 3.7 a Kasafin Kuɗin 2024.

Dakatar da Sanatan na zuwa ne bayan da aka yi wani zama da aka yamutsa hazo a zauren majalisar.

Wani mamba a kwamitin Kasafin Kuɗi a Majalisar Dattawa, Jimoh Ibrahim ne ya fara gabatar da ƙudirin dakatar da Sanata Ningi na tsawon wata 12, bisa zarginsa da ba da bayanai ba daidai ba waɗanda suke daidai da aikata babban laifi, da kuma hargitsa zaman lafiya a Majalisar Dokoki da ma ƙasar baki ɗaya.

Wasu ‘yan majalisar kamar Sanata Asuquo Ekpenyong sun goyi bayan ƙudirin Ibrahim ɗin.

Amma Ekpenyong, ɗan majalisa mai wakiltar Kuros Riba ta Kudu da kuma Sanata Abdulfatai Buhari daga Oyo ta Arewa, sun roƙi a rage tsawon dakatarwar zuwa wata shida da uku.

Akpabio, wanda ya bayyana laifukan Ningi a matsayin ‘manya’, ya gudanar da wata ƙuri’a da baki inda mafi yawan ’yan majalisar suka amsa amincewa da dakatar da Ningi na tsawon wata uku.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...