Manoma 4 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Nasarawa

0
142

Aƙalla mutum huɗu ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a ƙaramar hukumar Awe da ke jihar Nasarawa.

Aminiya ta gano cewa kwale-kwale da ke jigilar manoman shinkafa daga gundumar Ubbe a ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon, ya kife ne a wani kogi da ke ƙauyen Hunki na Ƙaramar Hukumar Awe a ranar Litinin da daddare.

Wakilinmu ya samu labarin cewa tuni aka kwaso gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa ƙauyen domin tantance su.

Waɗanda suka mutu sun haɗa da Alkali Congo, Shedrack Dauda, Mashack Dauda, da kuma Akolo Moses.

KU KUMA KARANTA: Kwale-kwale ya kama da wuta a Neja, yara biyu sun mutu

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Ramhan Nansel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Lafiya, babban birnin Jihar a ranar Talata, ya bayyana cewa har yanzu ba a gano direban jirgin ba.

Ya ce, “Lamarin ya faru ne jiya [Litinin]; manoman na dawowa daga gona lokacin da kwale-kwale ya kife.

“Amma an gano gawarwaki huɗu, kuma an ceto mutum ɗaya daga cikinsu.

“Sai dai har yanzu ba a gano matukin jirgin ba, amma ana ci gaba da ƙoƙarin gano shi.

Muƙaddashin Kwamishinan ’yan sandan jihar ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan su.”

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a baya-bayan nan mutum 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Kogi Kungra Kamfani da ke unguwar Arikiya a ƙaramar hukumar Lafia.

Leave a Reply