Mambobin ADC sun shigar da ƙara akan sabbin shugabannin riƙo na jam’iyyar

0
228
Mambobin ADC sun shigar da ƙara akan sabbin shugabannin riƙo na jam'iyyar

Mambobin ADC sun shigar da ƙara akan sabbin shugabannin riƙo na jam’iyyar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Mambobi uku na jam’iyyar ADC sun shigar da kara a gaban kotun tarayya da ke Abuja, suna kalubalantar shugabancin riƙon ƙwarya na jam’iyyar wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ke jagoranta.

A ranar 2 ga Yuni ne dai ƴan adawa su ka bayyana jam’iyyar ADC a matsayin wacce za su yi amfani da ita wajen hada kuri’u domin kau da Shugaba Bola Tinubu daga kan mulki a zaben 2027.

Ralph Nwosu, tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, ya ce shugabannin jam’iyyar a karkashin jagorancinsa sun yanke shawarar yin murabus tare da goyon bayan sabon shugabancin rikon kwarya.

Sabon shugabancin ya haɗa da David Mark da Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan jihar Osun, a matsayin shugaban riko na kasa da kuma sakataren riko, sai kuma Bolaji Abdullahi, tsohon ministan wasanni, da aka nada shi a matsayin kakakin jam’iyyar.

KU KUMA KARANTA: Jagoran PDP a Yobe, Adamu Waziri ya fice daga jam’iyar ya koma ADC

Sai dai a cikin ƙarar da su ka shigar, mai lamba FHC/ABJ/CS/1328/2025 a ranar 4 ga Yuli, wadanda suka shigar da karar — Adeyemi Emmanuel, Ayodeji Victor Tolu, da Haruna Ismaila — suna neman kotu ta tantance sahihancin shugabancin riƙon na ADC.

Sun bayyana cewa Ralph Nwosu ba shi da hurumin kiran zaman kwamitin ƙoli na ƙasa (NWC), ko kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar, ko wani zama, tun da wa’adinsa a matsayin kakakin ta na ƙasa ya ƙare.

Masu ƙarar sun kuma bayyana cewa shugabannin riko “ba za su iya ba kuma bai kamata su kasance a matsayin shugabanni ba,” suna mai cewa an naɗa su ne ta hanyar wani taro da tsohon shugaban jam’iyyar ya shirya ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply