Malaman firamare sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a Abuja

0
104
Malaman firamare sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a Abuja

Malaman firamare sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a Abuja

Malaman da ke koyarwa a makarantun firamare na gwamnati a birnin tarayya Abuja sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani.

Hakan na zuwa ne, bayan wa’adin kwanaki 14 da ƙungiyar malaman ta bayar ga ƙananan hukumomi 6 na birnin ya cika kuma ba a biya musu buƙatunsu ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa ɗalibai da su ka je makaranta a yau Laraba sun dawo gida inda suka ce malaman su sun koro su a yayin da su ka isa ƙofar shiga makarantar.

Da ya ke tabbatar da lamarin, shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa ,NUT, da ke Kubwa, Comrade Ameh Baba, ya ce an zauna tare da cimma matsaya kafin shiga yajin aikin.

KU KUMA KARANTA:Za mu kammala aikin layin dogo daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa ba – Gwamnatin tarayya

Ya ce sun dauki matakin shiga yajin aikin ne don tilastawa kananan hukumomin shida wajen cika alkawarin da suka dauka na biyan ariyas kaso 60 da suka rike.

Comrade Ameh ya yi Alla-wadai ga kananan hukumomin kan kin biyan alawus na kaso 40 ga Malaman da kuma kin karin albashi na kaso 25 da 35 ga Malaman.

Ya ce kasancewar ilim firamare shi ne tushe kamata yayi a bashi dukkan goyan baya da kulawa.

Kungiyar tayi gargadin cewa yajin aikin, yanzu ta fara.

Leave a Reply