Makauniyar masaƙiya na ɗaukar nauyin iyalinta da sana’ar saƙa tabarma

0
220

Cikin ƙwaryar Dar es Salaam, birni mafi girma a Tanzania, akwai yankin Chamazi inda Barati John take saƙa tabarma ta samu kuɗin ɗaukar nauyin kanta da ƴaƴanta huɗu.

Bahati John wacce aka fi sani da Mrs Khadija, ta gwanance ƙwarai wajen saƙa tabarma, ta irin baiwar da Allah ya yi mata, ta iya sarrafa abu da hannu, bayan ƙawayenta sun koya mata sana’ar tun shekarar 1994.

Ta gaya wa TRT Afrika cewa ta soma sha’awar saƙa ne tun tana ƙarama.

Wata rana, da ta gaya wa wata ƙawarta cewa tana sha’awar saƙa, sai ƙawar ta soma koya mata ta hanyar riƙe hannayenta sannan tana kwatanta mata yadda ake yi.

Bahati ta ce “Ƙawata ta fara koya min ta hanyar riƙe hannayena, saboda makafi suna aikinsu ne ta hanyar taɓa abu.”

“Ta gaya mini na saƙa kamar haka, wannan shi ne yadda mutane suke saƙa.”

Ƙasar da ke yankin Afrika ta Gabas tana fama da matsin tattalin arziki kama matasa sun bayyana damuwarsu game da rashin aikin yi. Amma Bahati ba ta taɓa ƙyale nakasarta ta kawo mata tarnaƙi wajen neman na kanta ba.

Sana’ar ta dogara ne da amfani da kaba kuma tana tsimin kuɗi daga cikin kuɗin da mahaifiyarta ta tanada don hidimar gida, ta sayi kayan aikin saƙa tabarmu.

KU KUMA KARANTA: Abun sha’awa: Yaro mai fuskar al’ajabi da shuɗin launin idanu

Bahati ta gaya wa TRT Afrika cewa ya danganci girman tabarmar, tana ɗaukar tsakanin makonni uku zuwa wata ɗaya ta gama saƙa tabarma ɗaya.

Uwar ƴaƴa guda huɗun ta ce har yanzu tana da ƴaƴa guda biyu masu zuwa makaranta waɗanda take ɗaukar nauyin da sana’ar tata.

“Idan na sayar da tabarmata, ina magance matsalolin da ƴaƴana ke fuskanta ne,” in ji Bahati.

Bahati ta bayyana wa maƙwabta ƙarara cewa, ba ta son a dinga tausaya mata saboda nakasarta.

Da sanyin safiya a kullum, tana barin gidanta ta tafi wajen aiki kamar kowa.

Leave a Reply