Makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial ta ba da hutun zangon farko, an gargaɗi ɗaliban da su kasance masu biyayya ga iyaye (Hotuna)

0
82

A yau juma’a ne makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial, Potiskum jihar Yobe, ta ba da hutun ƙarshen zangon farko a ɗaliban makarantar.

A lokacin ba da hutun, shugaban makarantar (Headmaster) Malam Muhammad Ibrahim Jaji ya yi nasiha a ɗaliban da su kasance masu ladabi da biyayya ga iyayensu.

KU KUMA KARANTA: Makarantar Hafsatu Gimba Ahmad ta halarci gasar ranar makarantu masu zaman kansu ta ƙasa

Hutun na sati Uku ne aka bayar, za a dawo makaranta ranar 5 ga Janairu 2026.

Tun da farko sai da ɗaliban suka yi taken ƙasa (Najeriya) inda suka rera sabon taken gwanin burgewa. Sannan Malama Fatima Ali Lawan ta rera musu taken makarantar mai daɗin gaske.

Leave a Reply