Makarantar ‘Hafsatu Gimba Ahmed Memorial’ an fara sayar da fom

0
104
Makarantar 'Hafsatu Gimba Ahmed Memorial' an fara sayar da fom

Makarantar ‘Hafsatu Gimba Ahmed Memorial’ an fara sayar da fom

Daga Ibraheem El-Tafseer

Makarantar ‘Hafsatu Gimba Ahmed Memorial’ da ke garin Potiskum jihar Yobe, ta fara sayar da fom na ɗiban sabbin ɗalibai.

Ita dai wannan makaranta, wanda fitaccen ɗan jaridar nan Dakta Hassan Gimba anipr, ya gina ta domin tuna wa da mahaifiyarsa Hajiya Hafsatu Gimba Ahmed, an mata tanadi na musamman domin ba da ilimi mai inganci ga ɗalibai.

Domin samar da ƙwararrun malamai, a ranar Lahadi, HGA Memorial, ta yi taron horas da Malaman makarantar domin ƙara sanin sauƙaƙan hanyoyin koyarwa a zamanance.

Malam Musa Yawale Mato (daga College of Administration Management and Technology, Potiskum) da Dakta Abdullahi Mamuda (daga Federal College of Education Technical, Potiskum), sune suka gabatar da jawabai a wajen.

An gudanar da taron ne a harabar makarantar da ke unguwar Jaji, kusa da sabon Shago Potiskum.

Makarantar HGA Memorial, makaranta ce da ta ƙunshi sashin Nursery da kuma Firamare, wanda yanzu haka an fara sayar da fom na Nursery 1, 2 da 3. Sai kuma fom na Firamare 1. Makaranta ce da aka mata tanadi don samar da ɗaliban da za a ba su karatu mai inganci, don su samu tushen karatu (foundation) mai kyau.

An samar da ƙwararrun malamai waɗanda za su koyar a fannoni daban-daban, ciki har da ɓangaren Islamiyya. A makarantar, an samar da kayan koyar wa na zamani, irin su kwamfuta, slate da sauran kayan koyar wa na zamani waɗanda za su sauƙaƙa wa ɗaliban wajen sauƙin fahimtar karatu.

KU KUMA KARANTA: Mawallafin jaridar Neptune Prime ya gina makaranta da asibiti a Yobe (Hotuna)

Sannan a makarantar HGA Memorial, za a karantar da sana’o’in hanu (skills acquisition), domin ɗaliban su koyi sana’o’in hanu iri daban-daban.
Za a samu fom ɗin a harabar makarantar da ke unguwar Jaji Potiskum jihar Yobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here