Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Hukuncin Kotun Umuahia Kan Dokar Zabe

0
349

Daga; Bashir Bello, Majalisa Abuja.

MAJALISAR dattawa Najeriya, ta bayyana damuwarta dangane da hukuncin da kutun tarayya ta garin Umuahia ta yanke inda ta ce sashe 84 karamin sashe na 12 na dokar zabe bai dace ba, sannan ta bayyana shi a matsayin wanda ya saba wa kundun tsarin mulki, kuma ya haramta bashi da wata fa’ida.

Majalisar ta bayyana cewa alkalin kotun yayin da yake yanke hukunci yace sashe na tamanin da hudun karamin sashe na 12 na dokar zaben ya ci karo da sashe na 61 karamin sashe na 107, da sashe na 137 da kuma sashe na 182 karamin sashe na 1 cikin baka na kundin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

A cewar majalisar wadannan sashe sashe na kundin tsarin mulki da alkalin ya dogara a kan su na nufin cewa babu wanda ya cancanci a zabe shi a kujerar majalisar dattawa, ko ta wakilai, da gwamna ko shugaban kasa idan har yana aiki da Gwamnatin Tarayya ko ta Jiha bai sauka daga mukamin shi kwanaki talatin kafi ranar zabe.

Sanata Sabi Aliyu shi ne matamakin babban mai tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya.

Sai dai Sanata Sani Musa daga Jihar Niger wanda kuma yana daga cikin masu takarar shugabancin Jam’iyyar APC ya fadawa Shugaban Majalisar dattawan da ya cire sunan shi a cikin jerin sunayen wadan da suka dauki nauyin gabatar da wannan kudiri.

Haka kuma Sashe na 84 karamin sashe na 12 cikin na dokar zabe ta 2022 ya bayyana cewa babu wani mai rike da mukamin siyasa da zai yi zaben deliget ko a zabe shi a matsayin deliget a babban zaben ko wace Jam’iyyar siyasa da nufin tsaida yan taraka a ko wane zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here