Mahara a Anambara sun ƙona fadar babban Basarake ƙurmus

0
203

A ci gaba da matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar jihar Anambara, rahotanni na cewa wasu ‘yan bindiga sun sake gudanar da mugun aiki a gidan wani Basarake a jihar.

Wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun bankawa gidan mai sarautar gargajiya wuta a jihar Anambra.

Mai sarautar gargajiyar a ƙauyen Isseke da ke ƙaramar hukumar Ihiala da ke jihar, Igwe Emmanuel Nnabuife ya tabbatar da lamarin.

Wannan na zuwa mako ɗaya bayan ‘yan bindiga sun sace direban tsohon gwamnan jihar, Chinwoke Mbadinuju, cewar Premium Times.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Sakkwato sun ƙona wata mata da ‘ya’yanta biyu da kuma surukanta har lahira

Lamarin ya faru ne yayin da ya ke gudanar da bikin binne ɗan uwansa da ya rasu a ƙauyen Isseke.

Rahotanni sun tabbatar cewa direban ya gagara biyansu kuɗaɗen su kafin binne ɗan uwan nasa inda suka farmaki gidansa da dare.

Maharan sun durfafi gidan nasa inda suka ta harbi a sararin samaniya yayin da suka ɗauke shi zuwa wani da ba a sani ba.

Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Igwe Emmanuel Nnabuife ya ce maharan sun ƙona masa gidansa ƙurmus.

Ya koka kan yadda aka kai masa farmakin inda ya ce ba shi da matsala da kowa a yankin da za a yi masa haka, cewar Tori News.

Ya ce:“Da gaske ne an ƙona mini gida kurmus wanda a yanzu haka na rasa komai da na sha wahalar nema a rayuwa, yanzu ba ni da gida.

“Komai ya ƙone amma nagode wa Allah babu rasa rai yayin lamarin da ya faru wanda ya tayar min da hankali.”

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Aderemi Adeoye ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka an fara bincike.

Leave a Reply