Magoya bayana su zaɓi jam’iyar ADC a zaɓukan cike-gurbi – Peter Obi

0
214
Magoya bayana su zaɓi jam'iyar ADC a zaɓukan cike-gurbi - Peter Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar LP, Peter Obi

Magoya bayana su zaɓi jam’iyar ADC a zaɓukan cike-gurbi – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya yi ƙira ga masu kaɗa ƙuri’a a Najeriya, musamman masoyansa na ƙungiyar Obidient da su zaɓi jam’iyyar ADC ne a zaɓukan cike gurbi da za a yi a ranar Asabar (16 Agusta).

Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, “a game da zaɓukan da za a yi a gobe Asabar, 16 ga watan 2025 domin cike gurbin wasu kujeru a jihohi 16 na Najeriya, tunda jam’iyyar LP ba ta da ƴantakara saboda kotu ta hana sanadiyyar rikice-rikicen da ke cikin jam’iyyar, ina kira ga masoyana da su su zaɓi jam’iyyar haɗaka ta ADC a jihohinsu.”

KU KUMA KARANTA: Zan yi haɗaka da sabuwar jam’iyyar ADC don a kayar da Tinubu, amma ba zan fice daga jam’iyar PDP ba – Sule Lamiɗo

Wannan jawabin na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara game da yunƙurin haɗakar siyasa, inda ake tunanin manyan jam’iyyun hamayya za su iya haɗuwa a guri ɗaya domin fuskantar Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Za a zaɓen ne a jihohi 16 a Najeriya, inda za a yi zaɓen cike gurbi na sanatoci biyu, da majalisar wakilai biyar da majalisar jiha guda 9 a jihohi daban-daban.

Leave a Reply