Ma’aikatan lafiya na Najeriya sun janye yajin aikinsu na kwanaki 12 bayan wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin.
Ƙungiyar ma’aikatan ta JOHESU, wadda ta yi ganawar da shugaba Tinubu, ta ce ta yanke shawarar janye yajin aikin ne domin bai wa gwamnati wa’adin mako uku domin shawo kan matsalolin da suke fuskanta.
Mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dakta Obinna Ogbonna ya ce “an samu ci gaba” a tattaunawar da suka yi da shugaban ƙasa.
“Amincewa tamkar abu ne mai haɗari, amma tun da a yanzu muna magana ne da sabon shugaban ƙasa, wanda da kansa ya roƙi mu ba shi lokaci, ya kamata mu ba shi.
KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya za ta shiga yajin aiki
“Bayan kwanakin 21 za mu duba inda ake sannan mu ɗauki mataki na gaba.” in ji Dakta Obinna a tattaunawarsa da BBC.
Ma’aikatan lafiyar dai na nema ne a yi watsi da tsarin biyan albashi na bai-ɗaya, da biyansu alawus-alawus ɗin aiki, da sake duba shekarun yin ritaya da dai sauran su.
[…] KU KUMA KARANTA: Ma’aikatan lafiya a Najeriya sun janye yajin aiki […]