Ma’aikatan jinya a Najeriya za su fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7

0
394
Ma'aikatan jinya a Najeriya za su fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7
Ma'aikatan jinya a Najeriya

Ma’aikatan jinya a Najeriya za su fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Unguwarzoma ta Ƙasa (NANNM) ta bayyana shirinta na fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a fadin ƙasa daga daren Litinin, 29 ga Yuli, saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen cika muhimman buƙatunta.

Ƙungiyar ta ce ta riga ta ba da wa’adin kwanaki 15 tun ranar 14 ga Yuli, amma gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya amince da ɗaukar ma’aikatan jinya 158, da ba da alawus ga ɗalibai 393

Shugaban ƙungiyar reshen babban birnin tarayya, Jama Medan, ya ce yajin aikin zai shafi dukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, na biyu da na uku a fadin ƙasar.

Daga cikin buƙatun ƙungiyar har da aiwatar da tsarin da aka amince da shi tun 2016, aiwatar da hukuncin kotu na 2012, ƙarin alawus ga ma’aikatan jinya da ɗaukar sabbin ma’aikata.

Ƙungiyar ta kuma bukaci a ƙirƙiri sashen jinya a ma’aikatar lafiya ta tarayya da kuma a janye sabon tsarin alawus da ta ce ya nuna wariya.

NANNM ta shawarci marasa lafiya da su nemi wata hanya ta samun kulawa yayin da yajin aikin zai gudana.

Leave a Reply