No menu items!

Sample Page Title

Date:

Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da rahoton sace mata ’yan gudun hijira kimanin 200 a Jihar Borno.

Majalisar ta soki sace ’yan gudun hijirar, wadanda yawancinsu mata ne, a Karamar Hukumar Ngala ta jihar.

Da yake tabbatar da cewa adadin ya haura 200, jami’i mai kula da harkokin jin kai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Malick Fall, ya “jajanta wa iyalai da dangin duk wadanda aka sace, musamman kananan yara, mata da tsofaffi.

“Sannan ina ƙira ga waɗanda suka sace su da su gaggauta sakin su ba tare da wani lahani ba.

“A madadin Majalisar Ɗinkin Duniya, ina tunatar wadanda ke wannan mummunan aiki da su kiyaye, su bari.

“Bugu da kari, ina kira ga hukumomi da sauran abokan hulda da su dubi yanayin rayuwar ’yan gudun hijira da ke sansanoni a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

KU KUMA KARANTA: An sace ɗalibai kusan 200 a ƙauyen Kuriga na jihar Kaduna

Jami’in Majalissar Ɗinkin Duniyan ya ce “A halin da ake ciki fiye da mutane miliyan biyu daga jihohin Borno, Adamawa da Yobe ne suke gudun hijira a makwabtan jihohinsu.

“Kwana biyu da bikin tunawa da ranar mata ta duniya wannan lamari na cin zarafi ga matan ya faru, wannan na tunatar da mu cewa mata da ’yan mata suna cikin wadanda wannan matsala tafi shafa,” in ji jami’in.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...