Likitocin ƙasar Saudiyya sun yi nasarar raba tagwaye ‘yan Najeriya da suka haɗe

0
417

An yi nasarar raba wasu tagwayen Najeriya guda biyu, Hassana da Hasina bayan an shafe sa’o’i 14 ana gudanar da aiki a ƙasar Saudiyya.

An haife su a ranar 12 ga Janairu, 2022, a Kaduna, Hassana da Hasina, sun haɗa ciki, ƙashin ƙugu, hanta, hanji, da hanyan fitsari da haihuwa duk suna manne.

Kamfanin dillancin labaran Arab News ya naƙalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ‘Arab News’ cewa, tawagar ƙwararrun likitocin mai mutum 85 sun kammala matakai bakwai daga cikin takwas na aikin tiyatar a asibitin ƙwararrun yara na Sarki Abdullah da ke birnin sarki Abdulaziz.

A ranar 9 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ne aka ɗauke tagwayen da iyayensu zuwa birnin Riyadh, tare da amincewar Sarkin don gudanar da raba su da kuɗin masarautar Saudiyya.

KU KUMA KARANTA: An haifi jariri na farko ta hayar IVF a Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya

Kafin a fara aikin, shugaban tawagar tiyata, Dr Abdullah Al-Rabeeah, mai ba da shawara ga kotun masarautar Saudiyya kuma babban mai kula da agajin jin ƙai na Sarki Salman da Relief Center ya ce aikin zai ƙunshi matakai takwas.

A baya dai ayyukan jin ƙai na Saudiyya sun taimaka da wasu tagwaye guda 130 daga ƙasashe 23 a cikin shekaru 33, kuma Hassana da Hassina za su kasance na 56 na tagwaye da za a raba a sakamakon haka, in ji Arab News.

Jakadan Najeriya a Saudiyya, Yahaya Lawal, ya gode wa shugabannin masarautar bisa irin taimakon da suka yi wa waɗannan tagwayen da suka haɗe da juna.

Leave a Reply