Libya ta kora ‘yan Najeriya da Mali 463 Zuwa Nijar
Kafin isar ‘yan ci-ranin a arewacin Nijar sun tagayyara a ƙasar Libya ciki har da mata da ƙananan yara sama da 100, inda ƙungiyoyin ayyukan jin ƙai suka nuna damuwa game da ‘yan Najeriya tare da yin ƙira ga hukumonin Nijar da su gaggauta ɗaukar matakan ɗaukar nauyin waɗannan mutane.
Ƙasar Nijar a duk rana ta na fama da kwararar baƙin haure daga arewacin ƙasar musamman waɗanda ake korowa daga Aljeriya.
An dai ce jami’ai sun ɓalle ƙofar wani gidan da wasu mutanen suke zaune tare da tafiya da su bayan kuwa kowannen su suna cikin gida sun shafe shekaru a ƙasar ta Libiya.
KU KUMA KQRANTA;Ƙasar Libya ta musanta shirin sayar da ɗanyen mai ga kamfanin Ɗangote
Suka ce jami’an sun ƙwace duk wasu shaidu da ke tabbatar da zaman su a ƙasar sannan kuma suka tsare su tare da mata kafin daga bisani suka jefa su cikin mutanen da aka tilasta musu fita ƙasar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama na ganin akwai buƙatar gwamnatocin ƙasashen yankin Afirka ta Yamma da su tura wata tawaga ta jami’ai domin tattauna yadda za’a bullo ma lamarin musamman tunda akwai dangantaka mai kyau tsakanin ƙasar Libiya da wasu ƙasashen na Afirka irin su Najeriya da Nijar.
To sai dai waɗanda aka koro na fatan samun ayyukan yi a ƙasashen su domin a cewar su rashin aikin yi ne ke sanya su waɗannan tafiye tafiyen zuwa wasu ƙasashen.