Lauyoyin Falasɗinawa sun shigar da Isra’ila ƙara a kotun ICC

0
214

Lauyoyin waɗanda hare-haren Isra’ila suka faɗamawa a Gaza sun shigar da ƙara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC da ke birnin Hague na Netherlands.

Wakilin jama’ar Gaza a kotun ICC wato Gilles Devers da wasu mutum huɗu da suka masa rakiya domin kai korafin sun bayyana cewa Isra’ila ta aikata laifukan yaƙi a kan Gaza waɗanda suka haɗa da kisan kare-dangi.

Isra’ila ta kashe sama da mutum 11,180 a Gaza waɗanda akasarinsu yara ne tun daga 7 ga watan Oktoba.

Leave a Reply