Labarin Mudi Sipikin da ɓarawo

1
334

Wata rana Malam Mudi Spikin ya dawo gida kawai sai ya hangi ƙofar gidansa cike da mutane ana ta hayaniya.

Nan da nan ya ƙarasa da sauri domin yaga me ke faruwa. Isar sa ke da wuya, ya tambayi wani mutum dake wurin, “me ke faruwa ne?” Mutimin yace masa ai ɓarawo aka kama ya saci buhun hatsi a gidan nan.

Malam Mudi yace “subhanalLahi!” A gidan nawa? Jin cewa shine maigidan yasa aka bashi wuri. Mutane kowa rike da makami, wasu na a miƙo shi mu gama masa aiki, wasu na a bari a kirawo ‘yandoka.

Malam Mudi na shiga soro, yace ina ɓarawon? aka ce masa gashi. Sai ya kalli ɓarawon, yace masa (cikin faɗa), “kai yanzu haka mu kayi da kai? Na gaya maka nima buhu guda ne ya rage min a gidan nawa, kuma ina da iyali, kuma ma ai cewa nayi in kazo kayi sallama, kace a auna maka rabin buhu, sai kawai kazo ka sunkuci buhu guda!” Nan kuwa Malam Mudi bai taɓa ganin ɓarawo ba.

Nan kuma jikin kowa yayi sanyi, wani maƙwabcinsa yace ma, malam Mudi, “dama kai ka aiko shi?” Wani kuma ya kalli ɓarawon, yace masa “kai ai sai kayi bayani, amma da kayi shiru, ai da tuni min gama maka aiki”.

KU KUMA KARANTA: Yadda Uba ya auri bazawara don nema wa ɗansa auren ‘yarta

Nan da nan malam Mudi ya sa aka kawo kwanon awo, ya farke buhun nan da ya rage masa, ya aunawa barawo kwana 20.

Ya kulle ya ɗaurawa barawon aka, har zai wuce, sai ya sanya hannu a aljihu ya ɗauko anini biyu ya miƙa masa, yace masa ga wannan in kaje kayi cefane, kasan uwargida sai da ɗan abin masarufi.
(Sai kace ya taba saninsa).

Tun daga ranar ɓarawon nan ya tuba da sata.

Kaico! Ko yau a Arewa zamu samu dattawa irinsu malam Mudi Spikin? Allah ya jikansa da gafara! Allah yajikan iyayenmu, Amin.

1 COMMENT

Leave a Reply