Labarin Haji Hassan na ƙasar Iran

0
555

Wannan hoton Haji Hassan, wani mai shago ne daga birnin Zanjan na ƙasar Iran.
Wani mutum ne ya ajiye kekensa a wajen Haji Hasan a matsayin ajiya, sai wani dalili ya saka wannan mutumi bai dawo ba.

Haji Hasan ya ci gaba da ajiye wannan keken a wajen shagon kowace safiya, sannan ya mayar da shi cikin shagon da daddare.

Wannan al’amari haka ya kasance har kamar tsawon shekaru 45, ana jiran mai keken ya dawo, amma bai dawo ba. Daga ƙarshe wata rana Haji Hasan ya rasu, amma mai keken bai dawo ba.

KU KUMA KARANTA: Labarin Mudi Sipikin da ɓarawo

Bayan rasuwarsa, gwamnatin ƙasar ta yi wani mutum-mutumi na wannan “Amin” da kuma keken tare da sanya shi a wani muhimmin mararrabar birnin domin ya zama misali na “Ahad-e-Wafa” wato riƙon amana da aminci.

Ya kake riƙe amana, idan an ba ka?

Leave a Reply