Kwankwaso ya ƙaryata zargin komawarsa wata jam’iyya

0
317
Kwankwaso ya ƙaryata zargin komawarsa wata jam’iyya
Dakta Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya ƙaryata zargin komawarsa wata jam’iyya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito fili ya karyata jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa ya mika wasikar neman shiga wata jam’iyya a Najeriya.

A cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a safiyar ranar Juma’a, Kwankwaso ya ce ba su taba aika irin wannan takarda ga kowace jam’iyya ba, inda ya bayyana labarin a matsayin ƙarya marar tushe.

KU KUMA KARANTA: NNPP ta nesanta kanta da shirin Kwankwaso na komawa APC

Ya shawarci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan jita-jita, tare da bin sahihan hanyoyin da aka kafa na ofisoshinsa domin samun sahihan bayanai game da harkokinsa na siyasa.

Kwankwaso ya kuma jaddada cewa duk wani bayani da ya shafi makomar siyasar sa za a sanar da shi ne ta tashoshin hukuma na musamman, ba ta hanyar maganganu a kafafen sada zumunta ba.

Leave a Reply