Kwankwaso ya yi ganawar sirri da Janar Babangida
Jagoran Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi wata ganawa da tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), a gidansa dake Hilltop, Minna, Jihar Neja, a yau Jumma’a.
KU KUMA KARANTA: Kwankwaso ya ƙaryata zargin komawarsa wata jam’iyya
A yayin ziyarar, Sanata Kwankwaso ya samu rakiyar Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dakta Ahmed Ajuji, inda suka gudanar da ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasar, kamar yadda mai taimakawa Kwankwaso a bangaren kafafen yada labarai, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook.









