Kwankwaso ya jagoranci addu’ar roƙa wa Abba nasara

0
245

Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taron addu’a na musamman a gidansa da ke Kano da safiyar Litinin.

An gudanar da addu’ar ta musamman ce domin roƙon nasara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a shari’ar zaɓen gwamnan Kano da ake Kotun Ƙoli.

Addu’ar da wata ƙungiyar ta Musulunci – Mu’assasatul Kwankwasiyya ta shirya ta gudana ƙarƙashin jagorancin Malam Yahaya Sufi, Malam Ashiru Nata’ala, Malam Bazallahi Nasiru Kabara da Malam Sadiq Isiyaku Rabi’u.

A yayin da suke gudanar da addu’o’in, Malaman sun yi addu’ar Allah ya ba Abba Kabir Yusuf nasara a kotun ƙoli da kuma Allah ya ba wa jihar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

KU KUMA KARANTA: Shirin gwamnatin Kano na gina sabuwar gada a Ɗan-Agundi ya tayar da ƙura

Taron addu’ar ya samu halartar jami’an Gwamnatin Abba Kabir Yusuf da masu riƙe da muƙaman siyasa da magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya.

Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne kotun ƙoli karkashin jagorancin wasu alkalai biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ta keɓe hukuncin bayan sauraron lauyoyin da ke kan lamarin.

Leave a Reply